A rika yi mana suka mai ma’ana – Sanata Wakili

Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa Malam Ali Wakili ya ce zai ci gaba da tallafa wa mutanen mazabarsa da kayayyakin more rayuwa, kuma babbar bukatarsa shi ne a dakile zaman kashe wando a tsakanin matasa.Sanata Ali Wakili ya ce tun lokacin da aka zabe shi yake tashi a zauren majalisar domin […]

A rika yi mana suka mai ma’ana – Sanata Wakili
A rika yi mana suka mai ma’ana – Sanata Wakili

Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa Malam Ali Wakili ya ce zai ci gaba da tallafa wa mutanen mazabarsa da kayayyakin more rayuwa, kuma babbar bukatarsa shi ne a dakile zaman kashe wando a tsakanin matasa.
Sanata Ali Wakili ya ce tun lokacin da aka zabe shi yake tashi a zauren majalisar domin gabatar da koke-koken mutanen mazabarsa duk da cewa akwai wasu sojojin haya da ya taimake su a baya amma daga bisani suka ce wai za su dawo da shi daga majalisar.
Sanata Ali Wakili ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Bauchi a karshen makon jiya. “Na raba kayayyakin karatu a makarantu 21 a Bauchi ta Kudu na sama da Naira miliyan 63 kuma na raba injinan ban ruwa ga kananan manoma sama da 300.Tun kafn a zabe ni Sanata nake alheri daidai bakin gwargwado, amma ba a rasa masu kananan maganganu na siyasa,” inji Sanata Wakili.
Sanatan ya ce duk da cewa aikin dan majalisa shi ne yin doka da za ta amfani kowa da kowa, amma ya tona bohol-bohol sama 20 a mazabarsa bayan zabensa duk da halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.
Ya ce ya kamata al’ummar mazabarsa su fahimci cewa ba ya da kudin da zan iya rabawa ga kowa da kowa amma duk inda hakkinsu yake zai bi sai ya karbo.
Sanata Wakili ya ce bai ce kada a soke shi ba, amma idan za a yi suka a yi mai amfani ba a yi don neman abinci kawai ba, inda ya ce Allah ne kawai Ya san abin da zai zamo nan da shekara ta 2019.
“Ina mutunta shugabannin Jam’iyyar APC tun daga matakin unguwa zuwa karamar hukuma zuwa jiha har zuwa kasa. Don haka babu wani dan siyasa da zai yi min barazana a siyasance,” inji shi.
Sanata Ali Wakili ya bukaci gwamnatocin kasar nan musamman na Arewa su bunkasa harkokin noma domin magance zaman kashe wando a tsakanin matasa tare da samar wa jihohin da kasar nan kudin shiga. “Idan aka bunkasa harkokin noma tabbas za a dakile zaman kashe wando da yawon roko a tsakanin al’umma domin kasar nan tana fama da karancin kudin shiga,” inji shi.