A rika yi wa barayin gwamnati afuwa bayan an kwace abin da suka sata ko a hada musu da dauri?

A makon jiya ne Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa ta kasa (ICPC) ta fara sanya barayin gwamnati amayo dukiyar da suka mallaka ta haramtacciyar hanya. Shin a kwace dukiyar ne kawai ko a hada musu da dauri? Na goyi bayan a rika hada nusu da dauri – Abdulkarim Alkali Daga Ahmed Garba Mohammed […]

A rika yi wa barayin gwamnati afuwa bayan an kwace abin da suka sata ko a hada musu da dauri?
A rika yi wa barayin gwamnati afuwa bayan an kwace abin da suka sata ko a hada musu da dauri?

A makon jiya ne Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa ta kasa (ICPC) ta fara sanya barayin gwamnati amayo dukiyar da suka mallaka ta haramtacciyar hanya. Shin a kwace dukiyar ne kawai ko a hada musu da dauri?

Na goyi bayan a rika hada nusu da dauri – Abdulkarim Alkali

Daga Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Abdulkarim Sa’idu Alkali: “Yakamata a rika hada wa barayin gwamnati da dauri ko bayan sun amayar da abin da suka sata.  Yin haka ne kurum zai zama darasi ga masu niyyar yin sata a nan gaba.  Mafi yawan masu satar suna dibar dukiyar ce a bisa mugunta don abin da suke dibar ya fi karfinsu da iyalansu yayin da suke barin mafi yawan al’umma  cikin tasku saboda haka bai kamata gwamnati ta yi musu wani sassauci ba.”

Hada musu da dauri ya yi daidai – Adamu Sele

Daga Ahmed Garba a Kaduna

Adamu Sani Abubakar:  “ Ina goyon bayan a kwato dukiyar da azzalumai ko barayin gwamnati suka wawure inda suka mayar da ita kamar gadon gidansu, sannan ina goyon baya dari bisa dari a hada musu da dauri bayan an kwato dukiyar don ya zama darasi ga ’yan baya.  Rashin garkame su a gidajen yari shi yake kawo wadansu ma su yi satar.  Duk da yake ba a bari a kwashe daidai amma a yi musu hukuncin dauri bayan an kwato dukiyar ya yi daidai.”

Idan aka kwace abin da suka sata a yi musu afuwa – Ali  Manzo

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe
 
Ali  Manzo Sarkin Doya: “Idan aka kwace kudin da barayin gwamnati suka sata ina goyon bayan da  ayi musu afuwa domin kada tashin hankalin ya yi musu yawa. Ka ga haka ko gaba za su yi taka tsantsan da dukiyar al’umma tun da ba tasu ba ce.”

Bayan an kwace abin da suka sata a daure su – Isa Teacher

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe

Muhammad Isa Teacher: “Ni ina goyon bayan idan aka kwace abin da barayin gwamntai suka sata a daure su saboda hakan ya sa wasu masu zuwa anan gaba su koyi darasi. Rashin dauresu bayan an kwace dukiyar da suka sata ta al’umma zai sa idan suka sake samun dama nan gaba su sake yin satar.”

A karba, a tura su gidan yari – Ustaz Tahir

Daga Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Ustaz Tahir Zubairu: “A gaskiya abin da nake ganin ya kamata ayi masu shi ne, bayan an kwace kudin da suka sace, sai a hada masu da hukuncin dauri a gidan yari domin ya zama darasi ga wasu masu sha’awar satar kudin gwamnati a nan gaba. Amma irin wadanda suka rike manyan mukamai da masu yawan shekaru ana iya yi masu sauki wato, bayan an kwace dukiyar da suka sace daga hannayensu sai a fallasa sunayensu ga duniya.”

Yakamata a hada musu da hukunci – Sani  Garba

Daga Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Sani Garba Fage: “Kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, tabbatar da hukunci ga barawo shi ne zai wanke shi daga zunubin da ya aikata. Saboda haka ina ganin idan har an tabbatar da laifin da irin wadannan mutane suka aikata na satar kudin gwamnati, to kamata ya yi a tabbatar musu da hukuncin da ya cancanci irin laifin da suka aikata. Idan har an yanke hukuncin daurin wata shida ga barawon kaza, me zai sa a kyale wanda ya saci kudi masu yawa da suke iya zama kasafin kudin wata kasa?”