A rika yi wa shugabanni kyakkyawar addu’a – Sabon Wazirin Kano
Sabon sarki Muhammad Sanusi , ya nada Alhaji Sa’adu Gidado daya daga cikin zuri’ar marigayi Sheikh Isa Waziri da ya rasu, a matsayin sabon wazirin na Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa nadinsa daga Allah ne. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Me za ka bayyana game da wannan mukami da ka samu?Waziri: […]

Sabon sarki Muhammad Sanusi , ya nada Alhaji Sa’adu Gidado daya daga cikin zuri’ar marigayi Sheikh Isa Waziri da ya rasu, a matsayin sabon wazirin na Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa nadinsa daga Allah ne. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me za ka bayyana game da wannan mukami da ka samu?
Waziri: Bismillahir Rahmanir Rahim, Alhamdu Lillahi Rabbil Alamin. Hakika sanda Allah Ya ba ni wannan matsayi na yi matukar godiya ga Allah, kasancewar na gaji abin da magabatana suka gada, kuma ina godiya ga dukkanin jama’a masoya dangane da goyon baya da soyayya da kauna da suka nuna mana. Muna gode wa kowa, Allah Ya saka da alheri.
Aminiya: Duk da cewa wannan abu ka gaje shi, amma da farko an nada wani a wannan mukami daga baya Ubangiji Ya canja al’amarin. Me za ka ce game da haka?
Waziri: To duk musulmi ya san cewa al’amura a hannun Ubangiji suke. Allah Shi ne mai bad a mulki ga wanda Ya so. Shi ne kuma Yak e karba daga hannun wanda Ya so. Ita wannan sarauta ta Wazirci kusan tana hannunmu zuriyar Wazirin Kano Gidado, tsawon shekara 105.
To amma lokacin da Allah Ya kawo wannan al’amari aka nada shi Waziri da ya gabata, Malam Nasir wanda ya yi kamar kwana hudu, to mun dauka cewa wannan abu kaddara ce, kuma mun karbi kaddara cewa al’amari ne daga Allah. To Allah cikin rahamarSa kuma Ya yi canjinSa, al’amarin nan ya sake dawowa hannunmu. Saboda haka dukkan godiya ta tabbata gare Shi.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga jama’ar Kano a kan wannan abin da Allah Ya wanzar a kanka da kuma shi Sabon Sarki?
Waziri: To abin da za mu yi kira ga dukkanin jama’a na Kano baki daya da dukkanin ma na sauran wurare, shi ne a bai wa shugabanni hadin kai. Mai martaba sarkin Kano da dukkanin sauran shugabanni da mu da muke mataimakansu, a ba d a hadin kai a kuma ci gaba da yi wa shugabanni kyakkyawar addu’a, domin kyakkyawar addu’ar nan ita ce za ta taimaka musu wajen gabatar da al’amura da za su ciyar da jama’a gaba. Don haka muna kira da a ba da hadin kai kuma a ci gaba da yi wa kasa addu’a domin a samu zaman lafiya.
Aminiya: Wadansu za su so su san alakarku da shi Wazirin da aka nada amma aka canja?
Waziri: To ba mu d a dangantaka ta jini da shi, amma akwai kyakkyawar alaka ta zamantakewa tsakaninmu da shi, tun da shi malamin majalisar sarki ne, ni ma kuma a lokacin ina malamin majalisar sarki. Shi yana limanci na waje, ni kuma ina rubutu na shari’o’i. Kasancewar dukkaninmu da ni da shi da ma sauran malamai da suke gaban majalisar sarki, duk muna karkashin ofishin Waziri ne. Don haka harkar aiki tana hada mu a kullum muna zama a gaban sarki tare, kuma sauran al’amura na yau da kullum suna hada mu muna zama. Akwai kyakkyawar alaka da fahimta.
Aminiya: Za nu so mu ji shekarunka da iyalanka?
Waziri: To ni a halin yanzu shekarata 48, an haife ni ranar 19 ga watan Yuni na 1966, kuma kasancewar ita sarauta ba koyaushe ne take zama a kan shekaru ba, abu ne Allah Shi yake bayarwa. Idan an duba wurare da yawa ga manya da yawa amma sai Allah Ya dauki mulki Ya bai wa karami. A halin yanzu akwai kannen mahaifina ma suna nan da rai. Akwai Alkali Badayi, wanda dan Wazirin Kano Gidado ne kuma kanin mahaifina ne, kuma an haife shi a 1920 ne, a halin yanzu shekararsa 94. Kuma malamin majalisar sarki ne a halin yanzu.
Akwai kuma dan uwansa Malam Zubairu Waziri wanda shi ma kanin mahaifina ne. Wadannan su ne biyu da suke rage daga cikin ‘ya’yan Waziri Gidado. Maganar yayye kuwa wadannan ma ba su da adadi, akwai jikokin mahaifina da suke girme ni duk yayye ne, sannan a gidanmu na Waziri Gidado ina da yayye guda biyu. Akwai Alhaji Shehu Waziri, ma’aikaci a Rediyo Kano, akwai kuma Alhaji Ali Waziri, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar kananan hukumomi. Sai kuma sauran ‘yan uwa gaba daya. Ina kuma da mace guda daya, yara kuma muna fatan Allah Ya ba mu.