A rike bindige barayin gwamnati – NLC

kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da takwararta ta kungiyar Manyan Ma’aikata (TUC) da kuma kungiyoyin kare hakkin jama’a sun bukaci a rika yanke hukuncin kisa ga ma’aikatan gwamnati da aka samu da almundahana kamar yadda ake yi a kasashen China da Indiya.kungiyoyin sun yi wannan kira ne a shekaranjiya Laraba a taron manema labarai da […]

A rike bindige barayin gwamnati – NLC
A rike bindige barayin gwamnati – NLC

kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da takwararta ta kungiyar Manyan Ma’aikata (TUC) da kuma kungiyoyin kare hakkin jama’a sun bukaci a rika yanke hukuncin kisa ga ma’aikatan gwamnati da aka samu da almundahana kamar yadda ake yi a kasashen China da Indiya.
kungiyoyin sun yi wannan kira ne a shekaranjiya Laraba a taron manema labarai da suka kira a Abuja.
Shugaban kungiyar NLC, Ayuba Wabba da ta TUC, Bobboi Kaigama, sun ce akwai bukatar a ci gaba da yaki da almundahan da rashawa a kasar nan. Kuma sun gudanar da gangamin nuna goyon baya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Alhamis kan shirinsa na yaki da almundahana da cin hanci da rashawa.
Mista Wabba ya ce kungiyar NLC tana goyon bayan duk matakin da za a dauka don kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar nan ciki har da hukuncin kisa.
“Idan za a rika kashe maciya hanci da rashawa a China da Indiya da Afirka ta Kudu, hakan zai iya faruwa a Najeriya; duk matakin da za a dauka don magance lamarin cin hanci da rashawa a kasar nan NLC za ta goyi bayansa,” inji shi.
Mista Wabba ya ce almundahana da cin hanci sun yi mummunar illa ga kasar nan, inda ya ce shugabbanin da ke mulkin kasar nan wajibi ne su zage damtse don ganin bayan wannan cuta mai ruguzawa. “A matsayinmu na kungiyar ma’aikata muna da yakinin cewa shugabannin kasarmu za su iya aiki wurjanjan don raba kasar nan da wannan mugun bala’i na hadamar tara abin duniya da wasoson dukiyarmu da aka rika yi ba kunya ba tsoron Allah a shekara shida da suka gabata,” inji shugaban kwadagon.
 kasa  Ya ce an hana galibin ’yan Najeriya samun ingantacciyar rayuwa sakamakon mugun cin hanci da rashawa da shugabanni ke yi, inda ya ce kungiyoyin kwadago ba za su sake zuba ido ana mulkin ganin dama a kasar nan ba. Ya ce kungiyar NLC tana goyon a kafa kotunan musamman don hukunta barayin gwamnati a kasar nan.
Mista Wabba y ace wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta tabbatar ta gano duk dukiyar da aka sace daga baitul malin kasar nan tare da gurfanar da wadanda suka yi hakan a gaban kotu. Sai ya yi kiran a samar da dokoki masu tsanani ga barayin gwamnati ta yadda za su zama firgitarwa ga masu tunanin aikata haka.
Shi ma Shugaban TUC, Mista Kaigama ya nuna damuwa kan yawaitar satar dukiyar gwamnati a matakan jihohi da kananan hukumomin kasar nan, inda ya ce abin takaici ne yadda lamarin ya kai wasu gwamnoni ba su iya biyan albashin ma’aikata na watanni. “Ba mu taba ganin an kasa biyan albashi har na wata takwas a cikin shekara 20 da suka gabata ba, wannan abin bakin ciki ne da tsabar almundahana ke haifarwa a kasar nan,” inji Kaigama.