A rushe kungiyoyin SOKAPU da Jama’a Foundation – Bishop Markus Dogo

Bishop din darikar Angilikan Bishop Markus Dogo ya ce mudddin ana son a samun zaman lafiya a yankin Kudancin Kaduna to ya kamata a rushe kungiyoyin SOKAPU da na Jama’a Foundation.                                                  […]

A rushe kungiyoyin SOKAPU da Jama’a Foundation – Bishop Markus Dogo

Bishop din darikar Angilikan Bishop Markus Dogo ya ce mudddin ana son a samun zaman lafiya a yankin Kudancin Kaduna to ya kamata a rushe kungiyoyin SOKAPU da na Jama’a Foundation.                                                    Bishop Markus Dogo ya bayyana haka ne a lokacin da wani ayarin Musulmi a karkashin kungiyar Gidauniyar Jama’a Foundation ya kai masa  ziyara a gidansa da ke Low Cost, Unguwar Garaje a garin Kafanchan. Ya  ce, tunda babu Musulmi a kungiyar da aka ce ta mutanen Kudancin Kaduna ce (SOKAPU) kuma babu Kirista a Gidauniyar Jama’a Foundation inda kuma a kowane lokaci suke musayar zafafan kalamai a tsakaninsu suna kishiyantar junansu. “Sai mun rushe su duka sannan mu zo mu dunkule a karkashin inuwa daya,” inji shi.  Bishop Markus Dogo, ya nuna jin dadinsa da ziyarar tare da yaba wa Sarkin Jama’a, wanda ya bukaci a kai masa ziyarar jajanta masa kan hadarin mota da ya samu, kuma ya nuna takaicinsa kan yaddda ake rayuwar hararar juna a tsakanin Musulmi da Kirista a Kudancin Kaduna sabanin sauran wurare.

Bishop Markus, ya bayyana rashin aikin yi a matsayin daya dage cikin dalilan tashe-tashen hankulan, kuma ya yi kira ga coci-coci da masallatai su rika yin ayyukan raya al’umma da taimakon jama’a ba sai sun jira gwamnati ta yi ba. “Na taba fada wa marigayi Bishop Bagobiri cewa mu fara yin wani abu don samar wa mutanenmu aikin yi, domin yawan surutu ba shi ne mafita ba. Ba komai ne za mu rika jiran gwamnati ba. Na tabbata za mu iya, domin abin da ake tarawa a coci-coci ranakun Lahadi sun fi karfin abin da karamar hukuma ke tarawa don haka za mu iya,” inji shi. Ya bayyana takaicinsa kan yadda mutum zai kashe dan uwansa. Sannan ya yi fatan dawowar zaman lafiya kamar yadda yake a baya a tsakanin Musulmi da Kiristan yankin. “A lokuta da dama idan ina fadakar da jama’armu wadansu cewa suke a rabu da ni, ni ban san abin da ake yi musu a yankin ba tunda daga Zariya nake,” inji shi.

A lokacin da yake bayyana makasudin zuwansu, jagoran ayarin, kuma Mataimakin Shugaban kungiyar Jama’a Foundation reshen karamar Hukumar Jama’a Malam Kabir Muhammad, ya shaida wa Bishop Markus cewa sun kai masa ziyarar ce bisa umarnin Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad don yi masa gaisuwa bisa hadarin mota da ya yi a kwanakin baya, da kuma yi masa addu’a da kuma karfafa shi a bisa irin wa’azin hadin kai da fadin gaskiya da ya ke yi ga kowane bangare kuma a kowane lokaci.

Bayan gabatarwar, Malam Hamza Ibrahim Na-Kawu ya yi takaitaccen jawabi kan hadin kai a tsakanin Musulmi da Kirista.

daya daga cikin wadanda suka yi jawabi, wani Bature, Dokta Les Martins, ya ce ya yi imani cewa dukan addinan biyu addinai ne na zaman lafiya sai dai ya nuna takaicinsa kan yadda wadansu daga cikin mabiya addinan suka gaza wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a tsakaninsu. “Dukaninmu ’ya’yan Ibrahim da Isa ne. Babu bambanci a tsakanin fararen fata da bakaken fata,” inji shi

Ayarin na mutum goma, ya kunshi maza bakwai da mata uku inda aka yi musayar lambobin waya don ci gaba da kulla zumunci sannan a karshe Malam Baba Tanko ya gabatar da addu’o’in samun lafiya ga Bishop din da kuma na samun zaman lafiya a tsakanin Musulmi da Kirista a Kudancin Kaduna da Najeriya baki daya.