‘A sake gina Arewa maso gabas maimakon ba da tallafin kudi’
Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fi mayar da hankali wajen farfado da ilmi da makarantun da ke shiyyar Arewa maso gabas, musamman idan aka yi la’akari da yadda rikicin Boko Haram ya daidaita ilmi da ilmantarwa a yankin, domin yanzu haka babu abin da wannan yanki ya fi kishirwa kamar ilmi, gyara hanyoyin yankin da […]
Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fi mayar da hankali wajen farfado da ilmi da makarantun da ke shiyyar Arewa maso gabas, musamman idan aka yi la’akari da yadda rikicin Boko Haram ya daidaita ilmi da ilmantarwa a yankin, domin yanzu haka babu abin da wannan yanki ya fi kishirwa kamar ilmi, gyara hanyoyin yankin da kuma kara jaddada tsaro, musamman yanzu haka akwai wasu kauyuka ma da ba su da makarantun boko; yayinda wasu ma a kasa suke daukar darasi.
Alhaji Saleh Suleman Jimeta, shugaban kungiyar ’yan kasuwa mazauna kasuwar Akim da ke Kalaba ne ya bukaci haka zantawarsa da Aminiya.
Ya ci gaba da cewa: “Tun da yanzu Allah Ya nuna mana lokacin da wadanda tilas ta sanya su kaurace wa muhallansu, yanzu suna komawa gida ga shi an lalata makarantunsu; akwai bukatar farfado da wadannan makarantu kuma ka da a yi sake wajen ci gaba da daukar tsauraran matakan tsaro. Matukar gwamnati ta yi haka, gibin da yankin ya samu ta fuskar ilmi zai cike sannan hanyoyin mota da suka lalace, muna so wannan gwamnati karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta gina su yadda harkokin kasuwanci za su farfado tare da bunkasa. Ta yin haka ne ’ya’ya da jikokin wannan yankin za su amfana, su mance da duk wata wahala da aka sha can baya.”
dan kasuwar ya ragargaji halayen wasu ’yan Najeriya na nuna gajen hakuri da matakan gyara da wannan gwamnati take dauka, musamman yaki da cin hanci da rashawa da kuma kwato kudaden da wasu da ya bayyana da masu yi wa kasa da al’umarta zagon kasa suka sace. Ya ce, ai kamata ya yi a yi hakuri, tunda ana gan in fa’idar canji na alheri da ’yan kasa suka yi mafarkin samu kuma Allah Ya tabbatar da shi.
Ya kara da cewa: “Mutane suna ba ni mamaki, barnar da shugabancin baya ya tafka tsawon shekara goma sha shida; yau koda gyaran gida mutum zai yi sai ya dan dauke shi lokaci kafin ya kammala, ina ga kuma na kasa gaba daya? Don haka kada ’yan uwana ’yan Najeriya su ci da zuci.”
Da yake yin tsokaci game da wadanda suka yi badakala a kudin sayo makamai, dan kasuwar ya bukaci wannan gwamnati da ta binciki tsohon Hafsan dakarun tsaron kasa, Aled Badeh. Domin a cewarsa, abin da ya ci doma ba zai iya barin awe ba. Ya kawo shawara gwamnati ta sake duba fasalin dokar hukunta wadanda aka kama da laifin cin amanar kasa, ko laifin yi mata zagon kasa. A kafa dokar da za ta sanya a rika yanke masu hukuncin kisa idan har hakan ta kasance.
Ya yi kira ga gwamnatin da ta sake duba batun tallafin Naira dubu biyar da ta ce za ta rika ba matasa. Maimakon haka, ta gina hanyoyi da asibitoci da kuma ilmi domin sai ’yan kasa sun wadatu da ilmi da kuma kula da lafiyarsu tukunna. “Samar da hanyoyin sana’a da ilmi za su fi bayar da kudin, domin wasu matasan na iya kashe zuciyarsu, ba tare da sun rungumi kasuwanci ko neman aikin yi ba. Za su mayar da kudin abin dogaro gare su.” Inji shi.