A samar da cibiyar horar da harkar yawon bude ido a Katsina

Gwamnatin Shema a Jihar Katsina ta yi kokari wajen kyautata halin da otal-otal din jihar suke, musamman ganin yadda ta daga darajar Katsina Motel, zuwa mai matsayi da kima irin na manyan otal din kasashen duniya. Kuma Malumfashi da Daura Motel duk an yi musu kyakkyawan gyara, ta yadda za a iya kwatanta su da […]

A samar da cibiyar horar da harkar yawon bude ido a Katsina
A samar da cibiyar horar da harkar yawon bude ido a Katsina

Gwamnatin Shema a Jihar Katsina ta yi kokari wajen kyautata halin da otal-otal din jihar suke, musamman ganin yadda ta daga darajar Katsina Motel, zuwa mai matsayi da kima irin na manyan otal din kasashen duniya. Kuma Malumfashi da Daura Motel duk an yi musu kyakkyawan gyara, ta yadda za a iya kwatanta su da manyan otal-otal na sauran jihohi, har ma na da na kasashen afirka da ke makwaftaka da mu. Wannan yunkuri na hukumar kula da otal-otal a Jihar Katsina, hakika abin a yaba ne, musamman ganin cewa yanzu mutane sun fahimci cewa harkar otal bat a holewa ba ce, tunda ko a biranen Makka da Madina akwai irin wadannan wuraren saukar baki.
Matukar mai girma Gwamna yana son al’umma jihar Katsina su ci gajiyar wadannan gyare-gyare da ya yi wa otal-otal a daukacin fadin jihar, dole ne a samar da cibiyar horar da kwararru kan harkokin yawon bude idanu da saukar baki da shirya girke-girke, na al’ada da na wasu kasashe da suka dace da zamani. Duk da cewa Mai girma Gwamna ya samar da dakunan taro a Motel, za a kara samun fa’ida idan har aka samar da dakunan karatu kanana a otal-otal din da ke fadin jihar. Domin yin haka zai bayar da dama ga masana da ke ayyukan nazarin bincike da wallafe-wallafe su samu wurin fakewa a otal-otal dinmu, sannan a tabbatar wa al’umma cewa otal ba wurin holewa kadai ba ne.
A kasashen duniya da ’yan Najeriya ke zuwa ziyara, musamman biranen Makka da Madina da Dubai, alhazan ke zuwa don ayyukan ibada da harkokin kasuwanci, kowa ya san harkar otal na cikin harkokin kasuwnci da ke bunkasa tattalin arziki. Don haka akwai bukatar a buga mujallu da kananan kasidu da za su baje kolin wuraren ziyara a birnin Dikko, musamman Durbi ta kusheyi da hasumiyar gobarau da Fadar Mai martaba sarakunan Katsina da Daura. Sannan akwai bukatar nuna wasannin gargajiya a akwatunan talabijin dinmu, ko allunan talla da ke daura da otal-otal. Aiwatar da irin wadannan dabaru za su kara samar da ayyukan yi ga matasa a fadin jihar Katsina, tare da kara samun kudin shiga daga masu kawo ziyara.
Duk da cewa Gwamna Shema ya yi matukar kokari wajen gyaran otal-otal a Jihar Katsina, kuma masu gani su yaba, sun yaba, ina ganin akwai bukatar Hukumar Otal-otal ta Jihar Katsina (Katsina State Hotel Board) ta rika fadakar da al’umma, har ma a cibiyoyin ilimi, kan muhimmanci gidajen saukar baki da shirya tarurruka da kebewa don nazarin bincike. Domin wannan zai sanya mutane su daina yi wa otal mummunar fahimta kan cewa wuri ne na badala da holewa da aikata masha’a.
Abin da kawai ya rage wa Gwamnatin Shema wajen kara inganta harkar otal da yawon bude ido a Jihar KAtsina, shi ne karya farashi ko saukake farashi ga ’yan asalin jiha da daliban makaranta. Sannan a bullo da tsarin tallata haja ga na kusa d ana nesa, a kafafen yada labarai da wurarren tarukan al’umma. Tunda Bahaushe y ace idan kana d akyau ka kara da wana, lallai akwai bukatar Malamai da masana a fannonin ilimi su bayar da udunmuwarsu kan yadda za mu kafa otal da ya dace da bukatun kowane irin addini da al’ada, don kauce wa badala da masha’a, tamkar yadda Gwmanatin Shema ta dauki hanya.
Irin wannan kokari na Gwamnatin Jihar Katsina, wajen inganta yanayin otal-otal, don bunkasa tattalin arziki da samar da aikin yi ga dimbin matasanmu, wajibi ne mutanen jihar su bayar da gudunmuwarsu ga gwamnati, ta hanayr bayar da shawarwari managarta. Idan jama’a suka sauke nauyin da ke kansu, ita hukuma za ta samu saukin sauke nata, don bunkasa tattalin arziki da siyasa da zamantakewa a wannan jiha tamu ta Dikko dakin Kara.
Hassanu Baban Gado F/Samji, Jihar Katsina

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno