A samar da kayan aiki ga sojoji don murkushe mahara – Tambuwal
Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nuna rashin jin dadi kan yadda Gwamnatin Tarayya ta fita batun sojojin kasar nan ba su da kayan aiki a kokarin da suke yi na kawo karshen tayar da kayar baya a kasar nan.Shugaban majalisar na magana da manema labarai ne a ranar Lahadin da tagabata bayan […]
Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nuna rashin jin dadi kan yadda Gwamnatin Tarayya ta fita batun sojojin kasar nan ba su da kayan aiki a kokarin da suke yi na kawo karshen tayar da kayar baya a kasar nan.
Shugaban majalisar na magana da manema labarai ne a ranar Lahadin da tagabata bayan ya karbi katin jefa kuri’a na dindindin a mazabarsa a makarantar firamare ta Jama’atu da ke garin Tambuwal a Jihar Sakkwato.
Alhaji Aminu Waziri ya nemi gwamnati ta ba sojojin hakkinsu yadda ya kamata domin su ji dadin kare martabar kasar nan. “Mutanen nan fa su ne aka dora wa alhakin kare martabar kasar nan. Ya zama wajibi mu ba su kwarin gwiwa ta hanyar samar musu da kayan aikin da duk suke bukata da kulawa da jin dadi da walwalarsu daidai gwargwado domin su kare kasar nan da kyau. Sojoji suna matukar kokarin kare al’umma da kasar nan baki daya, a makon jiya zan je Jihar Bauchi na bi kusa ga barikin sojoji abin da idanuwana suka gani ya tabbatar min cewa har yanzu ba a kulawa da jin dadin sojojin kasar nan,” inji Tambuwal.
Ya ce “A bangarenmu mun ba gwamnati hadin kai domin ta kawar da batagari, kan haka ne a duk lokacin da bangaren zartawa ya shirya kasafin kudi a fannin tsaro ba mu rage ko Naira, kuma mun yi wa dokar yaki da batagari gyaran fuska wadda ta ba gwamnati cikakken iko, amma duk da haka a kowane wata sai sun aiko mana suna son su yaki mayakan sunkuru.”’
Alhaji Tambuwal ya ce “Bai kamata a fake da abin da ke faruwa a wasu sassan kasar nan domin hana wa jama’a hakkinsu na gudanar da zabe ba. Ya ce, in har Jihar Yobe za ta iya gudanar da zaben kananan hukumomi lami lafiya, babu abin da zai hana Hukumar Zabe ta kasa gudanarwa.
“Kan maganar ko in ci gaba da zama a PDP ko na canja sheka zuwa APC ko na tsaya takara Gwamnan Jihar Sakkwato ko in nemi kujerar Shugaban kasa, a halin yanzu ina tattaunawa da jama’ata musamman na yankina , duk hukuncin suka yanke haka zan aiwatar,” inji Tambuwal.