A samar da wakilcin masu sana’o’in hannu a hukumar SMEDAN – AWAJ

Gamayya kungiyar masu sana’o’in hannu ta Jihar Jigawa, mai lakabin AWAJ ta bukaci a samu wakilcin masu sana’o’i a Hukumar Kula da kananan Sana’o’i ta SMEDAN daga daukacin jihohi 36 na kasar nan, kamar yadda uban kungiyar Alhaji Umar danHadeja ya bayyana wa Daraktan Hukumar Dokta Dikko Umar Radda. Sakatare Rabi’u Yakubu Sabaru da Malam […]

A samar da wakilcin masu sana’o’in hannu a hukumar SMEDAN – AWAJ
A samar da wakilcin masu sana’o’in hannu a hukumar SMEDAN – AWAJ

Gamayya kungiyar masu sana’o’in hannu ta Jihar Jigawa, mai lakabin AWAJ ta bukaci a samu wakilcin masu sana’o’i a Hukumar Kula da kananan Sana’o’i ta SMEDAN daga daukacin jihohi 36 na kasar nan, kamar yadda uban kungiyar Alhaji Umar danHadeja ya bayyana wa Daraktan Hukumar Dokta Dikko Umar Radda. Sakatare Rabi’u Yakubu Sabaru da Malam Shu’aibu Mai shari’a da dimbin ’yan kungiyar AWAJ ne suka rufa wa shugabansu da uban kungiyarsu baya a wajen ganawa da Daraktan Hukumar SMEDAN a Abuja, inda ’ya’yan kungiyar suka tabbatar da cewa su wakilai ne na birkiloli da masu faci da gyaran lantarki da gyaran famfo da masu turin kura da daukacin sana’o’in hannu da ake gudanarwa a Jihar Jigawa.
Shi kuwa shugaban gamayyar kungiyoyin masu sana’o’i na Jihar Jigawa Alhaji Ahmadu Ibrahim ya bayyana wa Daraktan SMEDAN makasudin ziyarar da suka kai masa a ofishinsa da ke Abuja. Ya ce ziyarar da suka kawo wannan ofishi na hukumar tallafa wa ci gaban kananan sana’o’i da masana’antu ta Najeriya, sun yi don gabatar da kungiyarsu da wakiltar daukacin masu sana’o’in hannu a Jihar Jigawa, sannan ya bukaci daraktan hukumar ya kara yi musu iso ga gwamnati jiharsu.
“Manufar ziyararmu ita ce mu nuna goyon bayanmu da farin ciki irin abubuwan da Gwamnati mai ci ta Muhammadu Buhari ta shirya yi wa masu sana’o’in hannu. Kuma muna son hukuma ta inganta alakarmu da gwamnatin Jihar Jigawa,” inji shi.
Shugaban Hukumar SMEDAN, Dokta Dikko Umar Radda, bayan da ya karbi kundin dokokin kungiyar, ya tabbatar suna da rajista a Jihar Jigawa, sai ya ce musu, ya yi matukar farin ciki da wannan ziyara da suka kawo masa, ya kuma ji bukatunsu, sai su sani hukumarsa ta fi mayar da karfi wajen bayar da horon sana’o’i ga kungiyoyi, ta kuma tsaya musu wajen samun rance kudin gudanar da sana’arsu, musamman idan suka zo a kungiyance.
“Na ji dukkan bukatun wannan kungiya ta masu sana’o’in hannu a Jihar Jigawa, amma ku sani cewa, mu a wannan hukuma ta SMEDAN mun fi bayar da karfi wajen horar da mutane su koyi sana’a, su san makamar tattalar dan abin hannunsu, har su bambance tsakanin uwar kudi da riba,” inji shi
Shugaban hukumar SMEDAN dai ya karkare bayanansa da yi wa ’ya’yan kungiyar AWAJ alkawarin duba bukatunsu, musamman in ya kai ziyarar aiki jiharsu. Sannan zai yi nazari kan yadda hukumar za ta samu wakilar daga masu sana’o’in hannu ko kafa kananan masana’antu a daukacin jihohi 36 da ake da su, tamkar yadda Alhaji Isyaku Umar ya gabatar masa a wajen wannan taro.