‘A samar mana da wuraren zuba bahaya’
kungiyar Masu sana’ar kwasar bahaya wacce aka fi sani da GIDAN KOWA AKWAI da ke Jihar Kano ta koka game da abin da ta kira ‘takurawa’ daga jami’an da ke kula da ababen hawa a jihar ke yi musu a duk lokacin da suke gudanar da sana’arsu. Sakataren kungiyar Malam Balarabe Yusuf ne ya yi […]
kungiyar Masu sana’ar kwasar bahaya wacce aka fi sani da GIDAN KOWA AKWAI da ke Jihar Kano ta koka game da abin da ta kira ‘takurawa’ daga jami’an da ke kula da ababen hawa a jihar ke yi musu a duk lokacin da suke gudanar da sana’arsu.
Sakataren kungiyar Malam Balarabe Yusuf ne ya yi wannan korafi lokacin da yake tattaunawa da Jaridar Aminiya.
Malam Balarabe ya bayyana cewa yawancin motocin da suke amfani da su ba motoci ne masu kyau wadanda za a ce dole sai an yi musu komai daidai da na lafiyayun motoci ba, “daga yanayin sana’armu kowa ya san ba yadda za a yi a dauki motoci masu kyau a saka a wanan harka. Yawancin motocin da muke amfani da su dama sun riga sun mutu, to irin su ne muke amfani da su. To mu kuma kasancewar dan abin da muke samu daga wanaann sana’a bai kai ya kawo ba (mun gode wa Allah) ba mu da abin da za mu yi wa wadannan motoci takardu. A wasu lokutan ma haya muke karbar motocin. A lokuta da dama idan muka fito aiki , sai ki ga wadannan jami’a hanya da suka hada da Jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra da bIO ba su yin la’akari da yanayin sana’armu sai ki ga sun tare mu, wai da sunan sun kama mu da laifi. Wani lokaci sai mun je ofis wallahi har sai mun biya tara. To kin ga wannan takurawa ce”.
Ya bayyana cewa tsawon shekaru 42 da aka kafa wannan kungiya gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ce kadai ta taba tallafa musu da motoci a duk gwamnatocin da ka yi a Jihar Kano. “Babu gwamnatin da ta taba tallafa mana sai ta Malam shekarau inda har ta ba mu motoci, duk da cewa a yanzu motocin sun mutu amma mun yaba abin da aka yi mana”
kungiyar ta nemi gwamnatin Jihar Kano da ta samar musu da wasu wuraren da za su rika juye bahayar da suka dauko kasancewar dukkanin wuraren da gwamnati ta ba su a baya, a yanzu jama’a sun mamaye wuraaren “ a yanzu haka yawanicn wuraren da muke kai wanan kaya mu zubar ya yi kusa da cikin al’umma. Kin san kullum yawa a ke kara yi to a yanzu mutane sun kusa kai wa irin wadancan wrare namu. Saboda haka muke neman a samara man da wasu wuraren can nesa da jama’a don mu rika harkokinmu ba tare da shiga hakkin mutane ba”
Sakatare Yusuf ya kara da cewa baya ga wannan bukata suna neman gwamnati ta tallafa musu da kayan aiki, musamman ma motar da suke amfani da ita wajen jigilar dauka tare da zubar da kashi. Ya bayyana cewa duk da cewa tsarin ginin masan zamani da ake yi a wannan lokaci ya dan rage musu samun yawan aiki amma hakan suke daukar nauyin kansu tare da iyalinsu gaba daya. “kin ga yanzu tsarin masan zamani na soccer way ya rage maan aiki haka kuma wasu suakn yi amfani da motocin zukewa , sai dai duk da haka muna samun aiki sai da ba kamar da ba”
Game da kyama da suke fuskanta daga al’umma sakataren ya bayyana cewa ba laifin jama’a ba ne yanayin sana’ar ne ya jawo musu hakan, don haka a cewarsa babu abin da za yi sai hakuri “babu shakka ana nuna mana kyama, duk da dia wasu sukan iya kokarin danne kyamarsu amma hakan ba ya boyuwa daga fuskokinsu. Koda yake wasu lokutan ba na ganin laifin mutane akan hakan , domin irin sana’armu ko mu ba don mun sami kanmu a ciki ba to mu ma hakan za mu yi. Ita wannan sana’a ce sai mutum ya hada da hakuri”
Har ila yau sakataren ya bayyana cewa suna daukar matakan kula da kansu ta hanyar tsaftace kansu bayan sun kammala gudanar da wannan sana’a tasu “yayin da muka fara wannan aiki za ki ga ba za mu taba sa hannu mu ci wni abinci ba har sai mun kamalla tsaf. Sai mun je mun yi wanka sosai tare da sanya turare sannan mu zauna mu ci abinci. Haka kuma muna neman magani a garajiyance kai har ma asibti muna zuwa mu gaya wa likitoci irin yanayin sanaarmmu indan ake rubuta magani don kulawa da lafiyarmu”.
Da yake bayani game da ci gaban da sana’arsu ta kwasar bahaya ta samu sakataren kungiyar ya bayyana cewa “ada muna amfani da amalanke wajen jigilar wannan kaya, to amma yanzu an samu ci gaba muna yin amfani da motoci, wanda yake ya fi tsafta”