‘A samar wa matasa aikin yi don a samu zaman lafiya’
Wani mai wayar da kan jama’a kan zaman lafiya da ci gaba, da ke zaune a Jos Jihar Filato, Alhaji Lawal Baba Otu ya ce akwai matasa marasa aikin yi sama da miliyan 23 a Najeriya, don haka ya zama wajibi a fito da hanyoyin sama musu abin yi. Alhaji Lawal Otu ya bayyana haka […]
Gwamna Simon Lalang na Filato
Wani mai wayar da kan jama’a kan zaman lafiya da ci gaba, da ke zaune a Jos Jihar Filato, Alhaji Lawal Baba Otu ya ce akwai matasa marasa aikin yi sama da miliyan 23 a Najeriya, don haka ya zama wajibi a fito da hanyoyin sama musu abin yi.
Alhaji Lawal Otu ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce babu yadda za a yi a samu zaman lafiya, idan ya kasance akwai miliyoyin marasa aikin yi a cikin al’umma. Ya ce don haka ne ake ta samun rikice-rikice a kasar nan.
Alhaji Lawal ya ce dole a kirkiro wa matasa ayyukan yi a kasar nan, matukar ana son a samu zaman lafiya. “Idan aka dubi wannan adadi akwai firgitarwa. Tabbas rikice-rikicen da suke faruwa a kasar nan rashin ayyukan yi ne ke kawo su. Don haka dole ne kasa ta tashi tsaye don magance wannan matsala” inji shi.
Ya ce hanyar da gwamnati ta dauka na rungumar harkokin noma a kasar nan da sake bude masana’antun kasar za ta taimaka wajen warware wannan matsala.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni su tallafa wajen samar wa matasa ayyukan yi, ta hanyar bude masana’antu da tallafa wa matasa wajen koyon sana’o’i.
Ya ce akwai wuraren koyon sana’o’i da dama a kasar nan da idan aka tallafa wa masu wuraren za su iya koya wa matasa sana’o’i.
Ya yi kira ga matasa su guji yarda ana amfani da su wajen tayar da rikice-rikice, su kama sana’o’i domin su taimaki kansu da iyalansu da kasa baki daya.