‘A sansanin gudun hijira na yi sakandare har na zama likita’

Yadda matasan Jihar Borno suka samu ilimi tare da cimma burinsu a yayin da suke zama a sansaninm’yan gudun hijira da ke Jihar Edo a yankin Kudancin Najeriya

‘A sansanin gudun hijira na yi sakandare har na zama likita’

Dakta Zachariah Timothy matashi ne dan gudun hijira daga Jihar Borno, wanda a sansanin ’yan gudun hijira ya yi karatu har zuwa jami’a har ya zama likita a halin yanzu.

Bayan tsallake rijiya da baya daga harin mayakan Boko Haram a kauyensu, Kughun a karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno ne matsahin mai shekaru 26 a yanzu, ya tsinci kansa a sansanin ’yan gudun hijira da ke Jihar Edo a Kudancin Nijeriya.

Duk da cewa rayuwar mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da garuruwansu a Jihar Borno ta zama abar tausayi, amma kwai abin sha’awa a game da matasansu, irinsu Zachariah Timothy, wadanda a hakan suka zama abin koyi wajen jajircewa da juriya a fadi-tashinsu domin kaiwa ga nasara.

Daidaita rayuwarsu da garuruwansu da Boko Haram ta yi da kuma halin da suka shiga bai sa sun karaya ba, domin kuwa a cikin sansanin ’yan gudun jihira suka yi karatu tun daga karamar sakandare har zuwa matakin digiri a fannin likitanci da hada magunguna da sauransu.

Yanzu burin Dakta Zachariah shi ne zama fitaccen likita mai tiyata a Nijeriya.

Shi da takwarorinsa sun bayyana irin halin da suka baro garuruwansu da yadda suka yi fama da tashin hankali da yunwa da talauci da kadaici da kuma burinsu a yanzu da suka zama lauyoyi da likitoci da injiniyoyi da manjoji da sauransu.

Aminiya ta bi diddigin labarinsu da yadda zama a sansanin gudun hijira ta sauya rayuwarsu da kuma yadda suka shawo kan manyan kalubale don cimma nasara a karatunsu. kaddara ta riga fata A lokacin da suka tsere wa Boko Haram, ba su da masaniyar irin sauyin rayuwar da za su fuskanta, musamman a sansanin gudun hijira da ke Jihar Edo, daruruwan kilomitoci daga jiharsu. Matasan, wadanda yawancinsu suka kammala digirinsu a shekarar karatu ta 2023/2024 sun ce ba su taba tunanin samun damar yin karatun jami’a a sansanin gudun hijira ba.

Tunaninsu a wancan lokacin kawai shi ne ganin samuwar zaman lafiya ba tare da jin karar abubuwan fashewa da harbe-harbe da guje-guje daga wani wuri zuwa wani ba, don tsira da rayuwarsu.

Mai kula da sansanin, Fasto Solomon, ya shaida wa Aminiya cewa fiye da dalibai 200 ’yan gudun hijira suna karatu a jami’o’i daban-daban, a yayin da 80 suka riga suka kammala karatunsu. Ya ce biyar daga cikin wadanda suka kammala karatun likitoci ne kuma suna neman wuraren aikin koyarwa (housemanship) a Abuja.

Sun bayyana wa Aminiya cewa sun guje wa rikicin Boko Haram ne don tsira da rayukansu, ba tare da sanin cewa wata kaddarar ce take tafe da su ba ta sauyin rayuwa.

‘A sansanin gudun hijira na yi sakandare har na zama likita’

Sansanin gudun hijirar Edo, wanda aka fi sani da ‘Home for the Needy’ da ke karamar Hukumar Obia ta Arewa maso Gabas a Jihar Edo, yana dauke da kimanin mutum 4,000, wadanda akalla kashi 90% dinsu sun fito ne daga yankin Arewa maso Gabas, musamman Jihar Borno. Sansanin na da makarantar firamare da sakandare ga ’yan gudun hijira da kuma yaran al’ummar yankin.

Ɗaya daga cikinsu, Zachariah Timothy, mai shekaru 26, wanda ya kammala karantun aikin likitanci, ya shaida wa Aminiya cewa ya zo Jihar Edo ne a shekarar 2015 bayan Boko Haram ta kai hari a garinsu.

“Bayan harin wanda ya girgiza ni sosai, dan uwana a Maiduguri ya nema min matsuguni a Jos, Jihar Filato. Daga nan aka sanar da ni game da wani fasto da ke taimakon ’yan gudun hijira a Jihar Edo,” in ji shi.

Ya ce ya tafi Edo a watan Satumba, 2015 inda aka sanya shi a aji uku na karamar Sakandare a sansanin, har ya rubuta jarrabawar WASC da NECO a shekarar 2018. Ya bayyana cewa abubuwan da ya fuskanta a sakandare sun shirya shi sosai don fuskantar rayuwar jami’a.

“A sakandare, ba mu da isassun ajujuwa; wasu daga cikinmu a karkashin bishiyoyi muke karatu kuma babu isassun littattafai. Wadannan abubuwa sun taimaka min wajen jure wa wahalhalun karatun jami’a. Na yi tunanin ba zan iya ba, amma bayan jarrabawar zangon farko, na gano cewa ashe ni ma ba ƙanwar lasa ba ne.

“Daga mataki na 300 zuwa shekarar karshe, biyan kudin makaranta a kan lokaci da samun kudin abinci ya zama kalubale, amma duk da haka, idan da na tuna abin da Boko Haram suka yi mini, da shawarar fastonmu kan jajircewa wajen karatu, sai na ci gaba duk da wahalhalun.”

Ya kara da cewa, duk da rashin kudi da abinci, ya kammala karatunsa ba tare da ya fadi wata jarrabawa ba, yanzu kuma likita ne.

A yayin da yake neman wurin yin aikin koyarwa (housemanship), burinsa shi ne ya gina asibiti a garinsu da kuma Jihar Edo wadda ta cika masa burinsa.

Burina zama Babban Lauyan Nijeriya —Saminu

daya daga cikin matasan da suka yi karatunsu na digiri a sansanin, Saminu Wakili Abacha, wanda ya kammala karatu a Fannin Shari’a daga Jami’ar Jihar Edo, Uzairue, ya ce burinsa shi ne ya zama Babban Lauyan Nijeriya (SAN).

Wakili, dan asalin garin Koghu a karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno, ya ce bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai kauyensu a shekarar 2014, “mun rasa matsugunanmu, sai muka fara gararamba don neman wurin kwanciya. Mun gudu zuwa Kamaru don samun tsira amma ba mu samu damar zuwa makaranta a can ba.”

Ya ce, yana Kamaru ne wani mutum da ya san Sansanin Gudun hijira na garin Benin ya kira shi, ya ba shi shawarar barin Kamaru. Mutumin ya dauke shi zuwa garin Benin a watan Janairun shekarar 2015.

Saminu Wakili ya ce, “Ina aji daya na Babban Sakandire (SS1) kafin rikicin Boko Haram ya kore mu, amma da na isa Benin, aka komar da ni aji biyu a karamar Sakandiri (JSS2). Na yi jarrabawa, aka dawo da ni SS1, sannan a SS3 na rubuta jarrabawar WASC da NECO na wuce, Kodayake sa biyu ina jarabawar jarrabawar.”

Ya ce, ba abu ne mai wuya, la’akari da abin da ya fuskanta a hannun Boko Haram, “amma na yi nasarar shawo kan tsoro da damuwar da ke a zuciyata bayan da mai kula da sansanin, Fasto Folorunsho Solomon, ya karfafe ni. A lokacin da nake sakandare a sansanin, ajujuwanmu ba su wadatar ba, wasu daga cikinmu muna karatu a karkashin bishiyoyi, idan aka fara ruwan sama, sai mu bar karatu mu dawo bayan ruwan ya lafa.”

Ya ce a jami’a ya fuskanci matsalolin kudi da abinci saboda yawan ’yan gudun hijirar da ke sansanin,

“Mai kula da sansanin ne yake da alhakin karatunmu, kuma saboda yawan dalibai a jami’o’i, muna fuskantar wahala wajen biyan kudin makaranta; wani lokacin ma ba mu samun kudin abinci a kan lokaci.”

Sakamakon haka, wani lokaci sai ya hakura da abinci, ya sha garin rogo kawai saboda ya san a makaranta yake.

“Na jajirce na fuskanci duk kalubalen da na samu don kammala karatuna a jami’a, saboda bayan rikicin Boko Haram ya raba mu da muhallinmu, ban taba mafarkin samun damar zuwa makarantar gaba da sakandare ba.

“Muna yin ayyukan da ba mu saba ba da su ba don samun kudi duk da wahalhalun da muke fuskanta, saboda koyarwar Fasto ita ce mu mayar da hankali kan karatunmu, shi kuma zai kula da sauran bukatunmu, kuma dole muka yi biyayya.

“Amma yau ni lauya ne, kuma ni ne dalibi mafi hazaka a sashenmu,” in ji shi.

‘Zan gyara kayan sadarwar da Boko Haram ta lalata’

A nasa bangaren, Alhaji Yusuf, mai shekaru 25, wanda ya kammala digiri a fannin Injiniyan Lantarki da Sadarwa daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya ce wata rana zai koma garinsu don gyara kayan aikin sadarwa da Boko Haram ta lalata.

Alhaji Yusuf, wanda ya kammala karatunsa da sakamako mai kyau, ya ce ya fara fuskantar wahala ne a watan Nuwamban shekarar 2014 lokacin da Boko Haram ta kai hari a garinsu, Gabba, da ke karamar Hukumar Gwoza, inda “Bayan harin, na koma wani kauyen makwabta tare da iyayena domin ci gaba da karatu a can, amma da Boko Haram suka aiko da wasikar barazanar kai hari a makarantarmu, sai aka tura mu gida babu shiri.”

Ya ce ba shi da matsuguni lokacin da ya ji labarin sansanin gudun hijira na Edo don haka ya yanke shawarar neman mafaka a nan. “Yanke shawarar barin yankinmu shi ne ya sauya tafiyar rayuwata gaba daya. Da na isa Edo a 2016, an yi mini tambayoyi, aka sa ni SS1, duk da cewa na kasance a SS2 kafin Boko Haram su raba ni da Borno. Na yi fice a SS1, musamman a fannonin kimiyya, sannan na samu karin ci gaba a SS2 da SS3.”

Ya ce ya rubuta jarrabawar WASC a lokacin da yake SS2 amma ya fadi a darussan Kimiyyar Halittu da Ingilishi, don haka ya sake a shekarar 2018, ya samu sakamako mai kyau, “Na kuma rubuta JAMB, aka ba ni gurbin karatu a Jami’ar ABU.”

Yusuf ya ce lokacin da yake jami’a, ya yi tunanin ba zai iya gogayya da takwarorinsa ba, “amma daga matakin 100 zuwa 400, na sami sakamako mai kyau kuma na zama dalibi mafi kwazo a sashenmu.”

Ya ce abubuwa sun yi masa wuya a jami’a, har wani lokaci mai kula da su dole ya rubuta wasika zuwa ga shugabannin makarantar don rokon su ba su damar rubuta jarrabawa duk da cewa ba su biya kudin makaranta a kan lokaci ba.

“Akwai matsalolin siyan littattafai da biyan kudin makaranta. A matakin 200, na rasa wani darasi a jarrabawar zangon biyu saboda yajin aikin ASUU. Na bar makaranta na koma sansani yayin yajin aiki, amma bayan an janye yajin, ban iya samun kudin komawa makaranta a kan lokaci don rubuta jarrabawar ba.”

Yusuf ya ce saboda wannan matsalar, ya kirkiro da tsarin cin abinci inda yake barin cin abincin rana har sai mai daukar nauyinsa ya turo kudin abinci.

“Amma, koyarwar Fasto Solomon ita ce, mu mayar da hankali kan karatunmu duk da wahalar da muke ciki, Allah Zai kubutar da mu. Don haka, dole muka jure wahalar don samun kyakkyawar makoma. Don haka, zuwa Sansanin Edo ya sauya rayuwata zuwa alheri. Yanzu, ni cikakken injiniya ne,” in ji shi.

Zan kare haƙƙin ɗan Adam — Riskatu

A nata bangaren, Riskatu Ali, mai shekaru 25 daga yankin Gabba na karamar Hukumar Gwoza, wadda ta kammala karatu a Fannin Shari’a daga Jami’ar Jihar Edo da ke Uzairue, ta ce ta tafiyar da ta kai ga zama lauya cike take da alheri da matsaloli.

“Lokacin da na fara, tsoron faduwa ya mamaye ni saboda na hadu da mutane daga wurare daban-daban, musamman wadanda suka yi makarantu mafi kyau na firamare da sakandare. Duk da haka, da kokari da jajircewa da karfin gwiwa na sami nasarar kammala karatu a cikin daliban da suka fi kwazo a sashenmu da sakamako mai kyau.

“Na wahala a makaranta; akwai matsalolin biyan kudin makaranta a kan lokaci da na samun kudin abinci. Wani lokaci, abokaina ke taimako na har sai wanda ke daukar nauyinmu ya turo mana kudin abinci.

“Na zo Jihar Edo a shekarar 2014 da tunanin hare-haren Boko Haram a garinmu a shekarar 2013. Na shiga cikin damuwa sosai domin wasu daga cikin dangina sun mutu a hareharen, na yi tunanin rayuwata ta zo karshe.”

Bayan ta koma Jihar Adamawa ne ta ji labarin Sansanin Gudun Hijira na Edo daga fastonsu wanda yi musu hanyar zuwa Benin a shekarar 2014.

“Na rubuta jarrabawar SSCE sau biyu; a karon farko na fadi wasu darussa amma a karo na biyu na ci duk darussa,” in ji Riskatu.

Ta ce a matsayinta na lauya, burinta shi ne ta zama babbar lauya wadda za ta kare hakkin marasa gata da mata.

Zan gina asibiti a Borno da Edo — Pharm Yabubu

A nasa bangaren, Yakubu Yusuf, mai shekaru 27, wanda ya kammala digirinsa a fannin Ilimin Magunguna daga Jami’ar Jihar Edo, ya ce “Zuwa Jihar Edo ya sauya rayuwata; nasarata ta fi abin da Boko Haram suka yi mini a Jihar Borno inda na rasa duk wani fata na zuwa makaranta.”

Yakubu, wanda ya zo sansanin bayan kammala sakandare, ya ce ya tsira daga harin Boko Haram tare da mahaifinsa amma ya rasa mahaifiyarsa da sauran ’yan uwansa ga ’yan ta’addan.

Ya ce “mun tsira ne saboda muna gona lokacin da suka kai hari a garinmu. Bayan harin, na koma wani kauye tare da mahaifina inda na yi ayyukan hannu don daukar nauyin kaina a makaranta har na gama sakandare. “Amma a nan Edo, mai kula da sansanin ne ke biyan kudin makaranta, shi ya sa na ce zuwana ya sauya rayuwata.”

Ya ce karatun jami’a babu dadi amma dole ya jajirce saboda wanda yake tallafa musu ya bayyana cewa yana tura su makaranta ne domin su yi karatu da samun nasara, ba don su kare a ayyukan hannu ba, “Don haka muka jure dukkan wahalhalun saboda mun san zai turo mana kuɗin abinci. Ina kuma da abokai nagari a makaranta wadanda suka taimaka min a lokacin tsanani.

“Wasu lokutan, nakan je aji ban ci abinci ba, amma duk da haka yau ni masanin hada magunguna ne, kuma ina godiya ga Fasto Solomon wanda, duk da bai san mu ba, ya karbe mu, ya ba mu masauki ya kuma dauki nauyin karatunmu.

“Wata rana, ina fatan komawa garinmu don bude asibiti da shagon magunguna da taimakon marasa galihu.”

‘Burin zama alkali’

Nethan Ibrahim, mai shekara 25 ya ce bayan ya kammala karatunsa na lauya a Jami’ar Jihar Edo, burinsa shi ne zama Babban Alkalin Nijeriya.

Ibrahim, wanda ya fito daga Arboko a karamar Hukumar Gwoza ta Borno, ya ce “Na rasa mahaifina a harin Boko Haram kuma a yayin da muke kokarin samun abin yi, suka sake kai hari a garinmu wanda wannan karon ya tilasta mana gudu baki daya.

“Mahaifiyata da sauran ’yan uwana sun gudu zuwa Kamaru, dan uwana na tagwaici ya gudu, ni kuma na gudu zuwa Maiduguri in da a nan na samu labarin sansanin nan da fasto ke taimaka wa ’yan gudun hijira, muka sami hanyar zuwa a 2015. un samu karatu da abinci da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sansanin, wanda duk ba mu samu a Borno ba.”

Ya ce ya fara karatu daga SSS II duk da cewa, saboda karancin littattafai, “wani zai karanta na awoyi kadan sannan ya miƙa littafin ga wani. Amma a karshe, na ci jarabawar WASC, NECO da JAMB na shiga Jami’ar Jihar Edo, don karantar aikin Lauyam, wanda na kammala da maki 4.32, na zama dalibi na biyu mafi hazaka da a tsangayarmu.

“Abin da na dauka da ba zai yiwu ba, yanzu yana hannuna. Na kammala da kyakkyawan sakamako kuma na kammala Makarantar Lauya a Kano.”

Na zama ƙwararren mai jure yunwa

Peter Isaac Mazhekwatte, mai shekara 27, wanda shi ma ya karanci lauya a Jami’ar Jihar Edo, ya ce yana jele daga wani kauye zuwa wani bayan Boko Haram sun kai hari a garinsu, Pulka, a shekarar 2012.

“Bayan harin, na biyo kawata zuwa Abuja don fara rayuwa a can. Na yi ayyuka daban-daban don in taimaki rayuwata da samun abin yi kuma a lokacin ne wani ya ce min zai je sansanin ’yan gudun hijira na Edo, sai kawai na tattara kayana na bi shi kuma hakan ne ya sa na samu kaina a Jihar Edo,” in ji shi.

Ya ce da farko sun wahala kafin su saba, amma sun yi mamaki yadda Allah Ya yi amfani da Fasto Solomon wajen gyara musu rayuwarsu.

Peter ya ce, “Tun daga farko, lokacin da na fara makaranta daga SSS I, na yi tunanin ba zan cim ma komai ba bayan Boko Haram sun kore mu, amma da himma, na fito da sakamako mai daraja ta biyu.

“A jami’a na zama kwararre wajen jure yunwa da wahalhalu saboda muna da yawa a jami’a kuma duk Fasto Solomon ke daukar nauyin mu. Tun da farko, mun san za mu fuskanci wahalhalu a jami’a kuma dole mu jure wa yunwa da sauran kalubale don samun kyakkyawar makoma,” in ji shi.

A gefe guda kuma, mai kula da sansanin, Fasto Solomon, wanda shi ne Babban Faston Cocin International Christian Centre da ke sansanin ’yan gudun hijira na Edo, ya ce ya gamsu da cewa yaran da suka zo sansanin ba tare da buri da wata fata ba yanzu sun zama kwararru masu shirin bayar da gudunmuwa ga al’umma.

Ya yi kira ga kungiyoyi masu bayar da tallafi na kasa da kasa da kuma mutane masu kishin kasa da su taimaka wa yaran ’yan gudun hijira.

Ya ce taimakon marasa gata yana daga cikin hanyoyinsa na bayar da gudunmuwa wajen ci-gaban al’umma da Nijeriya.

Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2

An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda

‘A sansanin gudun hijira na yi sakandare har na zama likita’

An dawo da wutar lantarki a Kaduna