A sanya Fulani da mahauta a cikin kwamitin Kano
Sarkin Fawan Agege-Legas, Alhaji Usman Musa Dawakin Kudu, ya ba kwamitin da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa na warware matsalar barayin shanu da masu shanun shawarar cewa akwai bukatar a kara yin hattara domin kauce wa kara wa mai karfi karfi ko kuma masu son zuciya.Ya bayyana haka ne yayin ganawa da Aminiya. Ya ce […]
Sarkin Fawan Agege-Legas, Alhaji Usman Musa Dawakin Kudu, ya ba kwamitin da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa na warware matsalar barayin shanu da masu shanun shawarar cewa akwai bukatar a kara yin hattara domin kauce wa kara wa mai karfi karfi ko kuma masu son zuciya.
Ya bayyana haka ne yayin ganawa da Aminiya. Ya ce kamata ya yi a rika shigar da wadanda suka san sirrin saniya, wato Fulatani da kuma mahauta, in dai har ana son warware matsalar kamar yadda ake yi halin yanzu, idan an kama barayin shanu.
Ya ci gaba da cewa kafa kwamitin da aka yi, kamata ya yi a tsoma Bafulatani da kuma mahauci amma sai aka sanya mutanen da ba su san sirrin saniya ba, aka ce masu shanun nan su zo su karba.
“Mai martaba Sarkin Kano, wakilansa da ya turo ba su san saniya ba, wakilan gwamna su ma ba su san saniya ba. Da ma wanda ya san saniya, daga Bafulatani sai mahauci.” Inji sarkin fawan na Agege.
Ya kara da cewa, matukar dai ana son a mika shanun ga masu su, to a rika sanya mahauta idan fa ana son dukiya ta koma wa masu ita.
“Wata hanya cikin sauki da za a iya tantacewa tsakanin aya da tsakuwa shi ne, shigo da Bafulatani. Hikimar ita ce, da zarar saniya ta ga Bafulani da aka sace ta a wurinsa, za ta gane shi, shi ma kuma zai gane saniyarsa.”
Daga karshe ya jinjina wa gwamnati da mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II bisa jajircewa da suka yi na yakar ’yan ta’adda da kuma ganin an yi hukunci daidai ruwa daidai kurji.