A sanya ido kan kungiyoyi

Editan Aminiya ka ba ni dama in tofa albarkacin bakina game da yunkurin ’yan majalisa na yin dokar da za ta sanya ido kan kungiyoyi. Idan dai kokarin da ake yi zai kawo tsafta a wajen gudanar da ayyukan kungiyoyin to muna goyon bayansa. Abi doka ka da ayi wa wasu bita-da-kulli. ’Yan majalisar Najeriya […]

A sanya ido kan kungiyoyi

Editan Aminiya ka ba ni dama in tofa albarkacin bakina game da yunkurin ’yan majalisa na yin dokar da za ta sanya ido kan kungiyoyi. Idan dai kokarin da ake yi zai kawo tsafta a wajen gudanar da ayyukan kungiyoyin to muna goyon bayansa. Abi doka ka da ayi wa wasu bita-da-kulli. ’Yan majalisar Najeriya dai na yunkurin yin doka domin sanya idanu ga kungiyoyin fararen hula da masu zaman kansu. A gaskiya na goyi bayan haka dari bisa dari. Domin sau da yawa mun sha ganin kungiyoyi masu labewa da kungiya suna aikata al’mundaha da cuta ga mutane. Kai har wasu na amfani da sunan kungiya suna barace-barace a kasashen waje da kuma wajen masu hannu da shuni! Rashin sanya ido akan ayyukan kungiyoyi shi ne ya kaimu ga matsalolin tsaron da muke ciki. Idan aka sanya idanu a kan ayyukansu hakika zai taimaka wajen sanin me suke aikatawa, kuma me suke gudanarwa. Sai dai kuma ya kamata sanya idon kada ya zama na wuce wuri ko kuma na wuce iyaka, wato ya zama kamar wani karfen kafa maimakon a samu ci gaba sai a samu ja baya. Ina fatan idan aka yi wannan dokar za ta taimaka wajen sanya wa kungiyoyi azama da jajircewa kan ayyukansu. 

Daga Ibrahim Rabilu Tsafe Jihar Zamfara. 07064282182  Ibrahim Rabilu <[email protected]