A sassauta dokar cire Naira 50

Hakika talakawan Najeriya sun kidima da jin dokar da Babban Bankin Najeriya CBN ya kafa na cire Naira 50 a kowace mu’amula da aka yi ta banki, matukar kudin ya kai Naira dubu. To, a gaskiya talakawan Najeriya suna kira ga Babban Bankin Najeriya da ma gwamnatin tarayya da su yi wa wannan dokar garanbawul […]

A sassauta dokar cire Naira 50
A sassauta dokar cire Naira 50

Hakika talakawan Najeriya sun kidima da jin dokar da Babban Bankin Najeriya CBN ya kafa na cire Naira 50 a kowace mu’amula da aka yi ta banki, matukar kudin ya kai Naira dubu. To, a gaskiya talakawan Najeriya suna kira ga Babban Bankin Najeriya da ma gwamnatin tarayya da su yi wa wannan dokar garanbawul kamar haka:
Da farko abin da ya kamata a yi, shi ne, kamata ya yi a ce duk wanda ya yi mu’amala da adadin kudin ya kai kamar dubu dari, shi ne ya kamata a ce an cire masa wannan harajin, amma adadin dubu 1000 daya ta yi kadan idan muka yi la’akari da bakin talauci da sama da mutum miliyan 100 suke fama da shi kuma kashi 90 cikin 100 na wadanda suke mu’amala da adadin dubu 1000 talakawa ne.
Kuma ai babu adalci a ce wai da wanda ya tura dubu daya da wanda ya tura biliyan 100 caji daya za a musu sam babu adalci a nan.
Kuma kamar yarda masana tattalin arziki suke zayyana mana a Najeriya ai akwai hanyoyi sama da dari (100) da Gwamnatin Najeriya za ta iya bi, domin kara adadin kudin shigar ta, ba wai sai an sanya wannan harajin ba. Kadan daga cikin hanyoyi sun hada da sayar da takardun kudi ( gobernment bonds ) da rage dogaro a kan man fetur, a kuma koma ga noma da kiwo da tono ma’adinan da Allah ya wadata mu da su. Saboda ta haka ne kawai gwamnati za ta kara adadin kudin shigar ta, kuma za ta iya sanya haraji ga hanyoyin manya manyan biranen Najeriya kamar Kano da Legas.
Daga karshen ina kira ga Gwamnatin Najeriya da ma Babban Bankin Najeriya (CBN) da su duba koken talakawan Najeriya a sassasauta musu wannan dokar. Saboda talakan Najeriya na fama da abin zai ci nema a yanzu.
Daga Salim Abubakar Imam Jingir dalibi a tsangayar nazarin tattalin arziki a jami’ar musulunci dake katsina kuma shugaban kungiyar muryar talaka reshen jahar filato 08067922200. Abubakar salim <[email protected]

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya