A sassauta dokar hana shigo da takin Kamfa – Kayarda

Wani babban manomi a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Alhaji Sani Umar Kayarda, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta sassauta dokar hana shigo da takin Kamfa daga waje, don magance karancin takin da manoman kasar nan suke fama da shi. Alhaji Sani Umar Kayarda ya yi wannan kira ne a lokacin […]

A sassauta dokar hana shigo da takin Kamfa – Kayarda

Alhaji Sani Umar Kayarda

Wani babban manomi a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Alhaji Sani Umar Kayarda, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta sassauta dokar hana shigo da takin Kamfa daga waje, don magance karancin takin da manoman kasar nan suke fama da shi.

Alhaji Sani Umar Kayarda ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce matakin da gwamnati ta dauka na hana shigo da takin Kamfa daga waje, bai dace ba. “Domin idan damina ta sake sauka babu takin Kamfa, manoma za su dada shiga cikin damuwa, domin aikin gona ba zai yiwu a kasar nan ba, dole sai da takin Kamfa,” inji shi.

Ya ce ya kamata gwamnati ta sassauta dokar hana shigo da takin Kamfa domin manoma su samu su bunkasa harkokin nomansu.

Alhaji Sani Kayarda ya ce ya kai shekara 25 yana noma kuma ya fara noman ne da noman masara daga nan ya rungumi kiwon kaji.

“Na fara noma masara buhu 14 ne, amma yanzu ina noma buhun masara sama da 1,000. Daga noman masara sai na rungumi kiwon kaji, idan na noma masara nakan nika, in yi abincin kaji ina bai wa kajin da nake kiwo,” inji shi.

Ya ce noman masara ne ya karfafa masa gwiwar rungumar kiwon kaji. “Domin idan kana noman masara, kana kiwon kaji ci bulus ne. Kuma akalla akwai mutum 50 da suke aiki a gidan kajina,’’ inji shi.