A sassauta harajin shigo da motoci – Kega

Shugaban Kungiyar Dillalan Motoci ta Najeriya reshen Jihar Filato, kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci na Kega Motors da ke Jos fadar Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega  ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta sassauta harajin shigo da motoci na kashi 70 da ta sanya kwanakin baya. Alhaji Yahaya Kega ya yi wannan kira […]

A sassauta harajin shigo da motoci – Kega

Alhaji Yahaya Muhammad Kega

Shugaban Kungiyar Dillalan Motoci ta Najeriya reshen Jihar Filato, kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci na Kega Motors da ke Jos fadar Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega  ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta sassauta harajin shigo da motoci na kashi 70 da ta sanya kwanakin baya. Alhaji Yahaya Kega ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa daAminiya a Jos, inda ya ce matukar harajin shigo da motocin yana nan kan kashi 70 cikin 100, akwai babbar matsala. “Domin  yanzu idan mutum ya sayi mota ta Naira miliyan daya, zai biya harajin Naira dubu 700 ne,” inji shi.

Alhaji Yahaya Kega ya nuna takaici kan yadda jami’an Kwastam suka rika zuwa da makamai suna rufe musu wuraren sayar da motocinsu, inda ya ce bai da ce a je ana  firgita mutane ana ba su  tsoro, kamar wadansu masu aikata miyagun laifuffuka da sunan ana neman  motocin da aka shigo da su ba tare da biyan haraji ba.

“Mu masu harkokin sayar da motoci ba masu aikata laifi ba ne. Wannan sana’a ce muke yi  muna da rajistar wuraren da muke gudanar da kasuwancinmu, kuma duk shekara muna biyan haraji. Jami’an Kwastam masu karbar haraji ne, kawai  ba jami’an tsaro masu yaki da aikata miyagun laifuffuka ba. Duk duniya babu inda ake karbar haraji da bindiga, ana karbar haraji ne da lalama’,’ inji shi.

Alhaji Kega ya yi kiran a sake  bude musu wuraren sayar da motocinsu da aka rufe, domin su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu.