A shekara 90: Yadda Allah Ya albarkaci Sheikh Dahiru Bauchi

Allah gafarta Malam mene ne takaitaccen tarihin rayuwarka? Assalamu alaikum wa rahammatullah. Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu. To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin […]

A shekara 90: Yadda Allah Ya albarkaci Sheikh Dahiru Bauchi

Allah gafarta Malam mene ne takaitaccen tarihin rayuwarka?

Assalamu alaikum wa rahammatullah. Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu. To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe. Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne. Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar  Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe. An haife ni ne a watan Janairun 1927 wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira a ranar Laraba.

Sunan mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adamu, shi mahaddacin Alkur’ani ne. Na rayu ne a hanunsa shi ya koya mini karatu har na haddace Alkur’ani a hannunsa. Sunan mahaifiyata Hajiya Maryam. Bayan na haddace Alkur’ani a hannun mahaifina ne ya tura ni duniya domin in je in gyara tilawata ta Alkur’ani. Na shiga duniyar Allah Ya taimake ni na gyara tilawar tawa, lamarin da ya sanya wadansu kan ce mini Gwani na Alkur’ani, wadansu mutanen kuwa kirana suke yi da Gangaran a fagen haddar Alkur’ani. Bayan nan sai mahaifina ya ce zai tura ni duniya in je in sake nemo ilimi, daga nan aka turo ni nan Bauchi domin neman ilimi. Na fara neman ilimi ban riga na samu ilimin da yawa ba, sai Allah ya sa Failar Shehu Ibrahim Kaulaha din nan ta bayyana. Dama mahaifina dan Tijjaniyya ne Mukaddami ne ta salsalar Umaru Futi, wato ta wajen Muhammadu Ghali. Kuma shi mahaifina ne ya ba ni darikar Tijjaniyya. Bayan da muka shiga Failar Shehu Ibrahim, sai ya zama kowace harka tawa sai ta hada da maganar Shehu Ibrahim. Alhamdulillahi na samu rabo mai tarin yawa a sha’aninsa, na soma yin tafsirin Alkur’ani ne a wajajen 1950, sannan na yi aurena na farko a 1948. Cikin alherin da Allah Ya yi mini, ’ya’yana tun suna kanana suke haddace kur’ani. Da farko ’ya’yana suna haddace kur’ani tun suna ’yan shekara 11, aka dawo 10, aka zo 9 har ya zamana cewa akwai ’ya’yana da suka haddace kur’ani suna ’yan shekara bakwai-bakwai da haihuwa. Ina da ’ya’yan da suka haddace Alkur’ani guda 70, kuma mutum uku ne kawai suka rasu daga cikinsu, wato Dokta Hadi da Ahmad da kuma A’ishatu (Yalwa) wacce ta rasu a hadarin mota a hanyar Yola amma sauran duk suna raye yanzu haka. 

Ta fuskar jikoki fa?

Alhamdulillahi, su ma suna da dama sosai. Ina da jikoki mahaddata guda 120 wadannan sun haddace Alkur’ani amma dukkansu suna da yawa sosai.

Ta fuskar iyali fa ko Malam nada mata guda nawa?

Matana hudu ne na kuma dade ina tare da mata hudu din nan, wadansunsu sukan tsufa sai su yi ritaya da kansu sai kuma na sake samun wadansu matan. Matana hudu ne a halin yanzu.

Mutane na mamakin dimbin ilimin da Allah Ya bai wa Malam ko akwai fannin da ya fi kwarewa?

Na farko bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne Alkur’ani. Daga nan kuma sai bangaren tafsiri, a nan malaman tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji su. Sai kuma bangaren Ma’arifa, ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiransa ilimin tarbiyya, a nan ma masu irin ilimi kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangare. Sauran ilimomi ina tattabawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da Tasrifi da Fikihu duk ina tattabawa. 

Jama’a na mamaki idan aka yi wa Malam fatawa sai ya hada da ba da misali maimakon gundarin amsar, ko me ya sa Malam yake yin haka?

Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane, idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su. Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen ba da amsa.

Ko Malam ya taba yin karatun boko?

(Dariya)…. Ai ko ABCD ban yi ba. Ni ban yi karatun boko ba, ko ABCD ban je na koya ba.

Ga shi Malam bai yi karatun boko ba ga kuma zamanin yau gwagwarmayar da boko ake hadawa ta yaya Malam yake yi?

Eh to, da yake muna tare da masu bokon, masu karatun na boko, wadansu ’ya’yanmu sun zama daktoci ba daya ba, ba biyu ba. Don haka suna dafawa wajen tafiyar da komai yadda ya dace. Muna da masu karatun boko sosai a cikin ’ya’yana da almajiraina kuma muna tare da su, ta haka muke gwagwarmayar rayuwar yau din.

Me Shehi ya fi sha’awa a rayuwarsa?

Abin da ya fi ba ni sha’awa, irin yadda na mayar da kur’ani sa’anata da kuma yadda na rungumi darikar Tijjaniyar nan ta zama rayuwata, kuma da dukanin wani mutumin da yake dangantuwa da son Annabi da son Allah ina sha’awar in sadu da shi. 

Me Shehi yake yi lokacin da yake hutawa baya karatun Alkur’ani ?

Wai! A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karanta Salatul Fatihi da Tasbihi da Istigfari da Salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori.

Wani irin abinci ne Malam ya fi sha’awa a rayuwarsa?

(Cikin matukar dariya)… Abincin Hausawa da Fulani su nake sha’awa, ina cin tuwon shinkafa, ina cin shinkafar ita kanta. To amma yanzu a halin da muke ciki na daina cin dawa da masara, na kuma daina cin tuwon masara da tuwon gero duk na daina cin su yanzu. Kuma babu wani likitan da ya hana ni cin su hankalina ne kawai ya ki su. Ka ga yanzu dai ina cin tuwon shinkafa da ita shinkafar kanta. Masara, tuwon masara, dawa, tuwon gero duk na yi ritaya da cin su a halin yanzu ba na cin su bisa ra’ayin kaina.

Ga shi yau za a yi taron zikiri da addu’o’in zama lafiya na sabuwar shekara kuma da safe Shehi ya yi magana a kai ko me Shehi ya ce?

Alhamdulillahi yau za mu yi taro na Zikirin Juma’a na wannan wata na farkon Shekarar Musulunci. A Almuharram, Juma’ar Farko mukan fara yi a nan Bauchi, Juma’a ta biyu mu yi a wani waje da na uku Juma’ar karshe na hudu kuma mu yi a Birnin Tarayya, Abuja. Daga yau za mu fara a nan Bauchi don Ubangiji Yana cewa: “La’ilaha illahu babbar katangaTa ce duk wanda ya shige ta ya huta da azabaTa.” Za mu gabatar da wannan La’ilaha illallahu mu sa Najeriya a cikin wannan babbar katanga Allah Ya kiyaye mu Ya kiyaye mana kasarmu daga dukan fitina. Kuma za mu fiskanci sabuwar shekara da La’ilaha illallahu sannan mu roki Allah Ya yafe mana zunuban da muka aikata a shekarar da ta wuce, abubuwan da muka yi na lada kuma Allah Ya karba. Sabuwar shekarar da muka shiga kuma Allah Ya sa mun shige ta da alheri ta zama shekarar alheri, shekarar zaman lafiya da kwanciyar hankali. A lokutan taron muna gayyatar dukan Musulmi domin La’illaha illallahu kayan dukan Musulmi ne mu zo mu yi zikiri tare a ji jawabai kuma a roki Allah tare. Allah Ya ba mu alheri Ya kiyaye sharri, fitintunun da suke faruwa Allah Ya yi mana maganinsu, bala’o’i duka Allah Ya kiyaye mana su. Kamar bala’o’in da muke fama da su na Boko Haram da satar mutane a nemi kudi da satar dabbobi da dukan bala’o’i Allah Ya yaye mana su, Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali.