…A shelanta afuwa ga ’yan Boko Haram – Shugabannin Addini
Shugabannin addini a karkashin kungiyar Tattaunawa a Tsakanin Addinai ta Arewa da kuma kungiyoyin Addinai ta Najeriya (Northern Inter Faith and Religious Organisations of Nigeria -NIFRON) sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta shelanta shirin yin afuwa na Shugaban kasa ga mayakan Boko Haram da ke zubar da jini a Arewa maso Gabas kamar yadda ta yi […]
Shugabannin addini a karkashin kungiyar Tattaunawa a Tsakanin Addinai ta Arewa da kuma kungiyoyin Addinai ta Najeriya (Northern Inter Faith and Religious Organisations of Nigeria -NIFRON) sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta shelanta shirin yin afuwa na Shugaban kasa ga mayakan Boko Haram da ke zubar da jini a Arewa maso Gabas kamar yadda ta yi wa mayakan yankin Neja-Delta.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Ko’odinetan kungiyar, Bishop Musa Fomsom na cocin Unlimited Mercy and Glory Church da ke Gombe da aka raba wa manema labarai, ta ce sakamakon nasarar da shirin afuwa ya samu a yankin Neja-Delta, akwai bukatar a yi haka a yankin Arewa da ke fama da hare-haren Boko Haram a yanzu.
Sanarwar ta ce, duk da cewa sojoji suna samun nasara a kan maharan, amma amfani da karfi kadai ba zai sa a samu nasarar yaki da ta’addanci ba.
Bishop Fomsom ya yaba wa kokarin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Neja-Delta kuma Ko’odinetan shirin Birgediya Janar Paul Boroh (mai ritaya) musamman kan yadda yake tafiyar da kudin shirin, ya ce, tuni ofishin ya horar da matasa dubu 17 da 322, saura dubu 12 da 678 da suke samun horo.
“Tun da ya karbi shugabancin shirin afuwar, Boroh ya dawo da kyakkyawar fata ga masu tayar da kayar baya. Kuma muna da yakinin idan aka samu irin wannan amintaccen mutum, irin wannan shiri zai samu nasara a arewacin kasar nan,” inji shi.
Bishop Fomson ya ce shirin yin afuwar ba ma zai dawo da zaman lafiya kadai ba ne a yankin, har ma zai karfafa samar da aikin yi ga matasa wadanda ake karkatar da su waje sanya su daukar makamai suna yakar kasarsu.
Ya ce galibin maharan an ci galaba a kansu, amma suna fama da rashin sanin makomarsu, don haka akwai bukatar a samu wanda yake da rikon amana don ceto su.
Ya bukaci gwamnati ta hanzarta ayyana shirin yin afuwar ta yadda za a sake gina yankin, musamman Arewa maso Gabas cikin gaggawa.