A shirye muke mu tattauna da Iran – Saudiyya
Wani babba a masarautar Saudiyya ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa a shirye kasarsa take ta tattauna kai-tsaye da abokiyar hammayarta a yankin wato Iran, muddin ta nuna cewa za ta janye dakarunta daga kasar Siriya.Yarima Turki al-Faisal ya ce kasashen biyu suna da abubuwa daya da za su iya gina wa […]
Wani babba a masarautar Saudiyya ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa a shirye kasarsa take ta tattauna kai-tsaye da abokiyar hammayarta a yankin wato Iran, muddin ta nuna cewa za ta janye dakarunta daga kasar Siriya.
Yarima Turki al-Faisal ya ce kasashen biyu suna da abubuwa daya da za su iya gina wa a kai.
Har ila yau, a yi marhabin da janyewar dakarun Rasha da yawa daga Siriya, kuma ya ce duk sojojin kasashen waje su ma su fice daga kasar.
Yarima al-Faisal ya kuma yi tsokaci a kan luguden wuta da sojin kasarsa ke yi a kasar Yemen, inda ya ce ba za a dakata da wannan aiki ba in har ‘yan tawayen Houthi da Iran ke goyon baya ba su yarda da tattaunawar zaman lafiya ba.