A shirye nake don karbar shawarwari- Shugaban alhazan Kaduna 

Sabon shugaban Hukumar Kula da Jindadin Alhazan jihar Kaduna Alhaji Sani Dalhatu Musa, ‎ya ce kofarsa a bude take domin karbar shawarwari da nufin ciyar da hukumar gaba. Ya ce, zai jagoranci hukumar tare da kowa da kowa domin a samu nasarar ciyar da hukumar Al’hazan jihar gaba da kuma jihar baki daya. Shugaban ya […]

A shirye nake don karbar shawarwari- Shugaban alhazan Kaduna 

Sabon shugaban Hukumar Alhazan jihar kaduna Sani Dalhatu Musa a dama yake karbar ragamar shugabanci a wajen Imam Hussaini Suleiman Tsoho Ikara

Sabon shugaban Hukumar Kula da Jindadin Alhazan jihar Kaduna Alhaji Sani Dalhatu Musa, ‎ya ce kofarsa a bude take domin karbar shawarwari da nufin ciyar da hukumar gaba.

Ya ce, zai jagoranci hukumar tare da kowa da kowa domin a samu nasarar ciyar da hukumar Al’hazan jihar gaba da kuma jihar baki daya.

Shugaban ya yi kiran ne a lokacin da yake karbar jagorancin hukumar a ranar Talatar nan da ta wuce a jihar.‎

” A shirye nake in karbi shawarwari a wajen ku kuma da taimakonku da goyan bayan ku Allah zai bamu nasara,” inji shi.

Ya kuma mika godiyarsa ga wanda ya karba a hannunsa tare da neman goyan bayansa domin ciyar da hukumar gaba.

Ya karbi ragamar mulkin ne daga hannun tsohon shugaban Hukumar Imam Hussaini Suleiman Tsoho Ikara. ‎