A shirye nake in bayyana a gaban kwamitin binciki – Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce binciken da Majalisar Dokokin Jihar ke yi a kan mukararraban bisa zarginsu da aikata almundahana a kananan hukumomin jihar 27 ba ya firgita shi ko kadan.Alhaji Sule Lamido ya fadi haka ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a garin Roni, inda halarci […]

A shirye nake in bayyana a gaban kwamitin binciki – Lamido
A shirye nake in bayyana a gaban kwamitin binciki – Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce binciken da Majalisar Dokokin Jihar ke yi a kan mukararraban bisa zarginsu da aikata almundahana a kananan hukumomin jihar 27 ba ya firgita shi ko kadan.
Alhaji Sule Lamido ya fadi haka ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a garin Roni, inda halarci wani bikin daurin aure, ya ce a shirye yake ya bayyana a gaban kwamitin bincike na majalisar domin kare duk wani zargi da za a yi wa gwamnatinsa. “Wadansu suna cewa ni barawo ne, na yi mulkin Jihar Jigawa tsawon shekara takwas na sace kudin jama’a. Don haka a shirye nake in je gaban kwamitin in amsa tanbayoyin da suke ganin za su yi min kuma koda za su gayyato min Hukumar EFCC ne domin bincika ta na shirya’” inji Lamido.
Alhaji Lamido ya kara da cewa “Duk abin da na yi wa jama’ar Jihar Jigawa har yanzu akwai
wadanda suke kirana barawo, an kira mu da ’yan Boko Haram an kira ni barawo, duk dai abin da kuka ga dama ku kira ni wannan wata manuniya ce cewa wasu gungun mutane a jihar ba sa ganin girman manya kuma su butulai ne ba sa godiya ga Allah.”
Ya ce wata rana gaskiya za ta bayyana a lokacin da kowa zai san gaskiya kuma jama’a su bambance barcin makaho.
A kwanakin baya ne Majalisar Jihar ta ba da sanarwar za ta tuhumi jami’an gwamnatin jihar tun daga kan Alhaji Sule Lamido har zuwa kan shugabannin kananan hukumomin jihar da ake zargin sun yi wawason dukiyar gwamnatin jihar.