A shirye nake in yi sulhu – Kim Jong-un

Kasar Koriya ta Arewa ta ce a shirye take ta dakatar da shirinta na makamashin nukiliya tare da yin shulhu.  Koriya ta Kudu ce ta ce Shugaban Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un ya bayar da hasken cewa zai so hawa teburin tattaunawa a kan rabuwa da makaman nukiliya idan har za a ba shi tabbacin […]

A shirye nake in yi sulhu – Kim Jong-un

Kasar Koriya ta Arewa ta ce a shirye take ta dakatar da shirinta na makamashin nukiliya tare da yin shulhu. 

Koriya ta Kudu ce ta ce Shugaban Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un ya bayar da hasken cewa zai so hawa teburin tattaunawa a kan rabuwa da makaman nukiliya idan har za a ba shi tabbacin tsaron kasarsa kamar yadda BBC ta ruwaito. 

Koriya ta Kudu ta ce an tattauna haka ne a yayin da jami’anta suka gana da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un a birnin Pyongyang.

Gwamnati a birnin Seoul ta kuma ce Koriya ta Arewa a shirye take ta gudanar da tattaunawa da Amurka kuma tana iya dakatar da gwaje-gwajenta na makamai masu linzami da na nukiliya. 

A can baya dai Koriya ta Arewa ta sha karya alkawuran da take dauka na dakatar da shirin nukiliyarta. 

Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2011, ba a taba sa ran Shugaba Kim zai iya barin kasarsa ba, ko kuma ya gana da Shugaban wata kasa hatta na China, kawa ta zahiri ga Koriya ta Arewan.

A watan gobe, Kim Jong-un zai yi wani taro da Shugaba Moon Jae-in a kan iyakar kasashen biyu mai tsananin tsaro. 

Ganawar za ta zama ita ce ta farko da za su yi a cikin shekaru da yawa.

Wannan al’amari ya zo ne sakamakon ganawa da Shugaban Koriya ta Arewa ya yi da wani ayarin jami’an Koriya ta Kudu, wadanda komawarsu gida ke nan daga birnin Pyongyang.

Wata sanarwa daga ofishin Shugaban Koriya ta Kudu ta ce “Arewa ta nuna son dakatar da shirinta na nukiliya a yankin Koriya. Idan ake dage barazanar soji da Arewar ke fuskanta aka kuma tabbatar mata da tsaronta, to ta ce ba ta da zabi illa janye aniyar tata.”

Dama dai Amurka ta sha cewa za a hau teburin tattaunawa ne kawai idan Koriya ta Arewar ta dakatar da shirinta nukiliya.

Shugaba Donald Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: “Duniya tana kallo kuma tana jira! Ko da ba da gaske ba ne, to Amurka a shirye take ta dauki duk matakin da ya dace.”

Yadda taron ganawar ya gudana

jami’an Koriya ta Kudu sun yi liyafar cin abinci ta tsawon sa’a hudu tare da Shugaba Kim Jong-un a ranar Litinin da ta gabata. 

Daga cikin ayarin akwai Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Koriya ta Kudu Suh Hoon da mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkar tsaron kasa Chung Eui-yong.

Hotunan da suka dauka sun nuna Mista Kim da bakinsa na Koriya ta Kudu suna cike da fara’a a teburin cin abinci. 

Haka akwai matar Mista Kim Ri Sol-ju, wadda ba ta faye bayyana a wuraren tarurruka ba, da kanwarsa Yo-jong, wadda da ita aka je Koriya ta Kudu lokacin gasar wasannin Olympics a watan jiya.

Ga dukan alamu dai kasashen biyu sun fara nuna alamun sasantawa da juna ne bayan kammala gasar Olympics, inda suka tsaya a karkashin tuta daya.