A shirye nake in yi zaman gidan yari – Diezani
Tsohuwar Ministan Man Fetur, Diezani Alion-Madueke, wacce hukumomin Amurka da Birtaniya da kuma Najeriya ke bincikar ta game da rub da ciki da ta yi da biliyoyin daloli a yayin da ta ke rike da mukamin ministar, ta ce a shirye ta ke da ta yi zaman kaso, sannan kuma ta sha alwashin tona asirin […]

Tsohuwar Ministan Man Fetur, Diezani Alion-Madueke, wacce hukumomin Amurka da Birtaniya da kuma Najeriya ke bincikar ta game da rub da ciki da ta yi da biliyoyin daloli a yayin da ta ke rike da mukamin ministar, ta ce a shirye ta ke da ta yi zaman kaso, sannan kuma ta sha alwashin tona asirin duk wanda ke da hannu cikin badakalar da ake tuhumarta.
A cewar ministar, bayan ta kammala bankadar asirin dukkanin wadanda suka hada kai wajen yin sama da fadi da biliyoyin dalolin, a shirye ta ke, a garkame su a gidan yari.
Kalaman tsohuwar ministar na kunshe ne cikin wani faifan da masu gudanar da bincike kan zargin da ake ma ta suka nada. Rahotanni sun ce tuni aka shigar da bayanan cikin bukatar ma’aikatar shari’ar Amurka, na neman kotu ta kwace kudi da kadarorinta da suka kai darajar dala miliyan 144.