A shirye nake na tattauna da Kwankwaso – Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana aniyarsa ta tattaunawa da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso game da matsalar shugabancin Jam’iyyar APC a jihar. Komawar Gwamna Kwankwaso APC, ta hura wutar rikici a tsakaninsa da Shekarau, sai dai yayin da Shekarau ke magana lokacin da shugabannin tsohuwar Jam’iyyar ANPP na kananan hukumomi 44 a […]

A shirye nake na tattauna da Kwankwaso – Shekarau
A shirye nake na tattauna da Kwankwaso – Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana aniyarsa ta tattaunawa da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso game da matsalar shugabancin Jam’iyyar APC a jihar. Komawar Gwamna Kwankwaso APC, ta hura wutar rikici a tsakaninsa da Shekarau, sai dai yayin da Shekarau ke magana lokacin da shugabannin tsohuwar Jam’iyyar ANPP na kananan hukumomi 44 a jihar suka kai masa ziyarar goyon baya, ya ce akwai bukatar shugabannin jam’iyyar daga sama su hada taro tsakanin shugabannin ANPP da ACN da CPC da Gwamna Kwankwaso don magance matsalar. Shekarau wanda tsohon dan takarar Shugaban kasa ne a ANPP a zaben shekarar 2011 ya ce ba shi da wani kulli tsakaninsa da wani dan Jam’iyyar APC ciki har da Gwamna Kwankwaso. Ya ce ba da kujera biyar daga cikin kujera tara ga Gwamna Kwankwaso abu ne da bai kamata ba, idan aka dubi rawar da ya taka wajen kafa Jam’iyyar APC.