A soke zaben fidda gwanin Jihar Sakkwato na PDP – Muntari Shagari
A wata tattaunawa da Aminiya ta yi Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Muntari Shehu Shagari, kwanakin baya. dan siyasar ya bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa da ya soke zaben fidda gwanin da aka yi a jihar da kuma kafa wani sabon kwamiti domin gudanar da sahihin zabe. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Me […]
A wata tattaunawa da Aminiya ta yi Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Muntari Shehu Shagari, kwanakin baya. dan siyasar ya bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa da ya soke zaben fidda gwanin da aka yi a jihar da kuma kafa wani sabon kwamiti domin gudanar da sahihin zabe. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me ye ra’ayinka kan zaben fidda gwanin da aka yi na jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato?
Muntari Shagari: Jama’a sun ga yadda aka yi rashin tsari mai kyau da ingantaccen haske, abubuwa ba su tafi dai-dai ba. Domin wannan zaben yakamata a kare shi fiye cikin sa’o’i hudu da suka wuce kawai, amma aka ki saboda ana son saka rashin gaskiya sai da aka kai karfe goman dare ba a fara zaben ba. Mutane sun yi ta koke da korafi, na samu wanda aka turo domin gudanar da zabe wato Sanata U. U Dukku, ba mu yarda da wannan yanayin ba saboda ni mutum ne mai son zaman lafiya da son wannan jam’iyya da jiha ta. Kuma ba mu son wannan jam’iyya ta tarwatse a jihar nan kan haka na yi kira gare shi da wannan zabe a dage shi zuwa wani lokaci domin a yi abin da yakamata masu zabe da jam’iyyar ta yarda da su yi an canja su da wasu daban, amma sai ya yi kunne uwar shegu damu.
Aminiya: Wasu za su ce kana wadannan kalaman ne saboda ka sha kayi?
Muntari Shagari: Ko daya, ba haka ba ne. Ni ne jagoran jam’iyyar a jihar nan. Na fi kowa son zaman lafiya a jihar nan wannan jam’iyya, ba wani mutum da ya fi ni sonta da wahala da ita na nuna mata soyayya ni mutum ne mai bin doka da oda kuma nasan jam’iyyar tana kan wannan turbar ban son abin da zai kawo mata cikas kuma ni ba zan sanya ido wani ko wasu su zo su lalata mana jam’iyya da muka wahala muka kafa ba. Saboda haka nake kira ga shugaban jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Adamu Mu’azu da ya soke kwamintin da ya gudanar da zaben fidda da gwanin gwamna a Jihar Sakkwato da kuma kafa wani sabo kwamiti domin gudanar da sahihin zabe da kowa zai aminta da shi.