A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu

Tinubu ya buƙaci INEC da jami’an tsaro su kasance na kowa.

A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su gudanar da ayyukansu cikin lumana da mutunta juna a yayin Zaɓen Gwamnan Edo da za a yi a gobe Asabar.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga.

Sanarwar ta ce Tinubu ya roƙi ’yan takarar gwamnan da jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su mutunta tsarin dimokuraɗiyya da kuma zaɓin mutane.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyya na bunƙasa ne a kan wayewa da juriya da haƙuri da kuma mutunta ka’idojinsa.

Da yake kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC da jami’an tsaro su kasance na kowa, Shugaba Tinubu ya ce dole kowane ɓangare ya gudanar da harkokinsa cikin lumana.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kasance cikin lumana da mutunta juna a yayin zaɓen.

Haka kuma, Tinubu ya umarce su da su warware kowace irin taƙaddama ta hanyar lumana ta hannun hukumomin da doka ta amince da su.

DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa

Sojoji da dama sun ɓace bayan harin Boko Haram a Borno

NFF ta naɗa Éric Chelle a matsayin sabon kocin Super Eagles

Abba ya nemi Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin Hajjin 2025