A taimaki ’yan gudun hijira!

Halin da miliyoyin ’yan uwana ’yan Najeriya ke ciki babu dadin ji, musamman a jihohin Barno da Yobe da Adamawa da  Bauchi da sauransu. Hakazalika da wadanda ke zaune a kasashe makwabta irin su Nijar da Kamaru da  Chadi da sauransu, duk a sanadiyyar hare-haren ’yan bindiga da tashin bama-bamai na kungiyar Boko-Haram.To hakika wadannan […]

A taimaki ’yan gudun hijira!
A taimaki ’yan gudun hijira!

Halin da miliyoyin ’yan uwana ’yan Najeriya ke ciki babu dadin ji, musamman a jihohin Barno da Yobe da Adamawa da  Bauchi da sauransu. Hakazalika da wadanda ke zaune a kasashe makwabta irin su Nijar da Kamaru da  Chadi da sauransu, duk a sanadiyyar hare-haren ’yan bindiga da tashin bama-bamai na kungiyar Boko-Haram.
To hakika wadannan miliyoyin jama’a da ke zaune a wadannan sansanonin ’yan gudun hijira su ma mutane ne kamar kowane  dan Najeriya, kuma suna da hakkin rayuwa mai kyau kamar kowa, amma abin lura shi ne; wane hali suke a yanzu? Yaya rayuwarsu ke kasancewa? Amsar ita ce suna cikin halin kuncin rayuwa na rashin iyaye ko ’yan uwa da rashin abubuwan more rayuwa. A duk lokacin da ka ji ko ka ga halin da ’yan gudun hijira ke ciki, to za ka ji matukar tausayinsu, kuma za ka yi alhini a kan halin da ka same su kuma za ka ji tsoron irin abin da ya same su kai ma ya same ka, sannan za ka ji haushin gwamnati da sauran masu hannu da shuni da suka ki taimakonsu.
Tabbas ’yan gudun hijira na kara shiga wani mummunan hali a lokutan da ake samun ruwan sama (damina) inda suke fama da cututtuka kamar amai da gudawa, da irin wannan lokacin na sanyi (hunturu) saboda matsalar abin rufa da sauransu. Hakazalika a lokacin zafi suna fama da matsalar cutar sankarau. Sannan ga babbar matsalar abinci da ruwan sha mai tsabta, ga matsalar ilimin ’ya’yansu da su kansu iyayen. A gaskiya halin da ’yan gudun hijira ke ciki a Najeriya da sauran kasashe abin tayar da hankali ne sai da Allah Ya kyauta.
A daidai wannan gabar zan yi amfani da damar in yi kira ga shugabannin da ke amsa sunansu na shugabannin duniya, da sauran masu hannu da shuni a fadin duniya, tare da gamayyar kungiyoyin sa- kai da na kare hakkin dan Adam da su kai dauki ga wadannan jama’a domin ceton rayukan talakawa.
A karshe zan yi kira ga Gwamnatin Najeriya da Shugaban kasa Muhammadu Buhari su kara kokari a kan wanda suke yi a yanzu na magance matsalar da ke haddasa gudun hijira, sannan wadanda ke cikin halin a yanzu a taimake su da wurin zama mai kyau da abinci da ruwan sha masu inganci, a inganta musu harkar kiwon lafiya; kuma a yi kokarin gyara musu muhallinsu, tare da mayar da su gidajesu na asali. Ina kira ga sauran al’umma da su rungumi ’yan gudun hijirar da Allah ya jarrabe su da wani al’amari na rayuwa, saboda kai ko ke ko mu ma ba mu fi karfin Allah Ya jarrabe mu ba, mu dauke su kamar yadda mutanen Madina suka dauki na Makka a lokacin da suka yi hijira. Ina adduaar Allah Ya sa wannan kira ta kai inda ta dace.
Adamu Aliyu Amo, Katsina. Sakataren kungiyar Muryar Jama’a, Reshen Jihar Katsina. 0909 730 0909

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno