A taka wa masu bai wa ’yan takara gudunmuwar kudi burki
A ranar Alhamis din da ta gabata shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yanki fom na neman ya sake tsawa jam`iyyarsu ta PDP takarar neman shugabancin kasar nan a cikin zaben shekara mai zuwa in Allah Ya kaimu. Tuni dai tarurrukanjiga-jigai da masu ruwa da tsaki na jam`iyyar ta PDP, suka amince da cewa shugaba […]
A ranar Alhamis din da ta gabata shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yanki fom na neman ya sake tsawa jam`iyyarsu ta PDP takarar neman shugabancin kasar nan a cikin zaben shekara mai zuwa in Allah Ya kaimu. Tuni dai tarurrukanjiga-jigai da masu ruwa da tsaki na jam`iyyar ta PDP, suka amince da cewa shugaba Jonathan shi kadai ne dan takarar jam`iyyar a cikin wancan zabe. Kodayake yanzu jam`iyyar ta sanya giyar ribas, har ta nemi wasu `yan takara biyu cikin neman shugabancin kasa a cikinta wadanda suka biya kudin sayen fom na takarar neman shugabancin kasar da ada ta hana masu fom da yanzu su zo su karba, wato dai ma`ana ta dade kofa. Masu neman takarar biyu su ne Alhaji Abdul Jelil Tafawa balewa da Uwargida Zainab Duke Abiola. Sai mu jira mu kuma roki Allah da Ya nuna mana yadda takarar ta su za ta kaya.
Abin da makalar tawa ta yau za ta mayar da hankali shi ne irin yadda Shugaba Jonathan a wajen yankar wancan fom ya iya kawo jerin sunayen wasu mutane wala-alla a zaman dai-dai ko ko a kungiya ce, kamar kungiyoyin mata `yan kasuwa da na dalibai da kungiyar gwamnonin jam`iyyarsa da na kare hakkin Bil adama, wadanda ya ce sun fito daga dukkan shiyyoyi shidda na kasar nan, wadanda ya ce su suka tara dari da kwabo har kusan Naira miliyan 100, suka kuma damka masa don ya sayi fom din neman takarar.
Ya ci gaba inda ya dauki lokaci ya bayyana jerin sunayen mutane da kungiyoyin da suka ba shi waccan gudummuwa da yawan kudin da suka bayar kamar haka:- kungiyar gwamnonin PDP Naira miliyan 22, Naira miliyan 2 a zaman Nagani-Ina-so, sai kuma Naira miliyan 20, a zaman kudin yankar fom, ita ma kungiyar Jakadun goyon bayan takararsa, wato TAN gudummuwar Naira miliyan 22, suka damka masa.
Shugaba Jonathan ya yi amfani da wannan dama wajen yin godiya da jinjina ga dukkan wadanda suka ba shi wannan gudummuwa yana mai cewa “Ina mai matukar godiya da karamcin da suka nuna mani. Ina kuma mai gode muku da farko akan yarda da kuka yi da kasar nan sannan da amincewa da kuka yi da jam`iyyar PDP, tunda dai kun riga kun sani fom din na takara a PDP ne, daga karshe kuma ina mai godiya da amincewar da kukai mani.” In ji shugaban kasar. Ya kuma ba da tabbacin cewa da zarar ya kai ga nasara, to kuwa zai tafi da kowa da kowa, yana mai jaddada cewa ba wani shugaban kasa komai dimbin ikonsa da zai iya canja al`umma shi kadai ba, dole sai da sa hannun kowa da kowa.
Ba wai shugaba Jonathan kadai ba jama`a da kungiyoyi suka taru suka tara wa kudi ba, don ya shiga wannan takara ta zabubbukan shekarar 2015, a can Jihar Kaduna ma a cikin makon da ya gabata al`ummar mazabar dan Majalisar Dattawa ta Kaduna ta Arewa na jam`iyyar APC suka tara sama da Naira miliyan 3, wanda suka saya wa dan takarar neman wannan mukami, kuma tsohon shugaban Kwamitin riko na jam`iyyar APC a Jihar Dokta Hakeem Baba-Ahmed. A can Jihar Zamfara ma labari ya yadu a cikin kas, inda aka ce masu bukata ta musamman (Nakkasassu), sun saya wa Gwamnan jihar, Alhaji Abdulaziz Yari fom na shiga wannan takara.
Haka labarin yake a Jihar Akwa Ibom, inda ya zuwa yanzu wasu matasa sun riga sun tara kudi sun kuma saya wa gwamnan jiharsu Mista Godswill Akpadio fom din a tsayawa takarar neman mukamin dan Majalisar Dattawa. Shi ma Gwammnan Jihar Binuwai, Dokta Gabreil Suswan kungiyar dalibai `yan asalin jihar da ke karatu a kasashen waje suka bayyana aniyarsu ta bakin Sakatare Janar dinsu Mista Terkaa Jam, wajen tara dari da kwabo don saya wa gwamnansu fom din tsayawa takarar dan Majalisar Dattawa a zabe mai zuwa.
Ba da gudummuwar kudi ga `yan siyasa a zamanin takara ba wani sabon labari ba ne, don kuwa koda a kasar Amurka inda muka aro tsarin mulkinta da muke jarrabawa, jama`a dai-daiku da kungiyoyi kan tara dari da kwabo don taimaka wa dan takarar da ransu ya kwantamawa, don ya kai ga nasara. Za ka taras kuma bil-hakki da gaskiya a bayyane ake yin komai, ta yadda kungiya ko mutane dai-daiku ba sa ba da abin da ya shantake tanadin dokar yin hakan. Sabanin mu a nan kasar duk wadannan tsare-tsaren basa aiki. Alal misali ina hankali zai iya dauka a ce da kai da kungiyar gwamnonin jam`iyya na ba da gudummuwar makudan kudi ga shugaban kasar da ke kan karagar mulki, don kawai ya sayi fom din shiga takara, kai ka san kudin talakawa aka dauko aka ba shi, in kuma ranar zabe ta zo nawa kowane gwamna zai kawo don samun nasarar shugaban kasar.
Haka batun yake a `yan kungiyoyin kasar nan, ka dauki kungiyar TAN, kungiyar a `yan kwanakin nan ta gama rangadin shiyyoyin kasar nan tana tattara wa shugaba Jonathan sa hannun`yan kasa da suke nemansa ya tsaya takara, har ta yi ta gama tana tare da Sakataren gwamnatin tarayya Sanata Pius Ayim Pius, wanda ba sai na fada ma yadda ta yi wancan rangadin gangamin neman goyon bayan jama`ar, amma yanzu ita ake cewa ta bada Naira miliyan 22, don saya wa shugaban kasa fom. Akwai kungiyoyin mata `yan kasuwa da na matasa da na dalibai, wadanda su kan su masu neman tallafin ne idanu bude airin wannan zamani, amma wai suma sun kawo nasu ajon.
Dadin-dadawa inda za ka gane bada gudummuwar duk giri ce da kara daure wa cin hanci da rashawa gindi da wannan gwamnatin ta kasa yaka, me ya hana da aka samu gudummuwa daya da ta isa a sai fom din aka kuma ci gaba da karbar na wasu. Ko kusa ba mamakin faruwar haka ga shugaban kasar da yake cewa “Sata ba cin hanci da rashawa ba ce.”
Samun wannan dama daga jam`iyya mai mulki wadda ita ya kamata ta tsawatar shi ya sa sauran jam`iyyu su ma su yi, don haka za a zama ba mai tada wani. Nasan a tanade-tanade Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, akwai yawan kudin da aka amince wa kowane mai neman takara ya kashe a cikin yakin neman zabensa, don haka tun daga yanzu ya kamata Hukumar ta INEC ta fara lissafin irin kudin da suke shiga hannun masu neman takara da kuma daga inda suke, ta yadda za ta iya maganin wannan mummunar annoba da take ruguza mulkin dimokuradiya. Yanzu ne kuma ya kamata ta sa idanu. Allah Ka ba mu ikon zaben shugabanni nagari da za su yi mana adalci tun daga sama har kasa, ba `yan gangan ba ko `yan tamore.