A Takaice…11
FIFA ta gargadi Brazil Sakatare-Janar na Hukumar FIFA Jerome balcke a ranar Talatar da ta wuce ne ya gargadi kasar Brazil a kan shirye-shiryen da take na daukar nauyin Gasar Cin Kofin Duniya da za a fara a watan Yuni mai zuwa.Sakataren ya nuna bacin ransa ne a lokacin da ya kai ziyarar ba-zata a […]
FIFA ta gargadi Brazil
Sakatare-Janar na Hukumar FIFA Jerome balcke a ranar Talatar da ta wuce ne ya gargadi kasar Brazil a kan shirye-shiryen da take na daukar nauyin Gasar Cin Kofin Duniya da za a fara a watan Yuni mai zuwa.
Sakataren ya nuna bacin ransa ne a lokacin da ya kai ziyarar ba-zata a daya daga cikin filayen wasannin da ake ginawa inda ya tarar da sauran aiki alhali lokacin fara gasar na karatowa.
Nan take ya nuna badin ransa kuma ya dibar wa kasar wa’adin makonni hudu zuwa ranar 18 ga watan Fabairun watan gobe ko kuma kasar ta fuskanci fushin hukumar.
Sai dai Sakataren ya yi fatan kasar za ta kammala ayyukanta a kan lokaci kafin a fara gasar.
Brazil dai ta shiga rudu ne ganin yadda kasa da wata biyar a fara gasar har yanzu ba ta kammala wasu daga cikin filayen wasannin ba.
Juan Mata zai koma Manchester United
Ga dukkan alamu dan kwallon kulob din Chelsea da ke Ingila Juan Mata ya kusa canza sheka zuwa kulob din Manchester United kamar yadda wata majiya daga kuob din biyu suka shaidawa kafar sadarwar ESPN a shekaranjiya Laraba.
Rahoton ya ce ana sa ran dan kwallon zai sanya hannu a kulob din United kafin karshen wannan mako.
Rahoton ya kara da cewa tuni jami’an kulob din United suka ziyarci Landan don ganawa da jami’an kulob din Chelsea a yunkurinsu na dauke Mata. Haka kuma ana sa san kulob din United zai dauke dan kwallon kulob din Jubentus da ke Italiya Arturo bidal kafin a rufe kakar saye da sayar da ’yan kwallo a watan nan da muke ciki.
Kulob din United dai ya shiga zawarcin zaratan ’yan kwallo ne bayan ya shiga matsalar rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a kakar wasa ta bana.
An sanya siyasa a zaben Gwarzon dan kwallon Duniya -Ribery
Shahararren dan kwallon kulob din Bayern Munich da ke Jamus dan kasar Faransa Franck Ribery ya koka kan yadda Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta gudanar da zaben Gwarzon dan kwallon Duniya a makon jiya.
Ribery yana daga cikin ’yan kwallo uku da suka fafata a gasar watau Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da kuma shi kansa.
Ya ce ya kadu matuka yadda aka zabe shi a matsayi na uku bayan Ronaldo da Messi sun samu kuri’un da suka dara nasa.
“Ta yaya za a ce bayan na samu nasarar lashe manyan kofuna biyar a kakar wasan da ta wuce alhali Ronaldo bai lashe ko kofi daya ba ya samu kiri’u fiye da nawa ba tare da an sanya siyasa a ciki ba?”
dan kimanin shekara 30, Ribery, ya kuma nuna bacin ransa a kan yadda hukumar FIFA ke yawan fifita gasar rukuni-rukuni na La-Liga da ke Sifen fiye da kowace gasa a fadin duniya, al’amarin da ya sa mafi yawan ’yan kwallon da ke lashe kyautar suke fitowa daga Sifen.
Ya ce idan aka lura daga cikin ’yan kwallo 11 da hukumar ta zabo wadanda ta karrama a kakar wasan da ta wuce shida daga ciki sun fito ne daga Sifen yayin da uku kacal suka fito daga Jamus duk da kungiyoyin kwallon kafar Bayern Munich da na Borussia Dortmund ne suka fafata a wasan karshe na gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a bara.
Idan za a tuna, Lionel Messi ne wanda ke kwallo a kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya lashe kyautar Gwarzon dan kwallon duniya (FIFA Ballon d’Or) sau hudu a jere yayin da Ronaldo dan kwallon Real Madrid na Sifen ya lashe ta bana.