A takaice: (20)

Manchester City ta fara zawarcin Pogba a kan Yuro miliyan 100 Kulob din Manchester City na Ingila ya fara zawarcin dan kwallon tsakiya a kulob din Jubentus da ke Italiya Paul Pogba a kan zunzurutun Yuro miliyan 100 kwatankwacin Fam miliyan 73.8. Rahoton da kafar watsa labaran wasanni ta Gazetteta dello Sport ta kalato a […]

A takaice: (20)
A takaice: (20)

Manchester City ta fara zawarcin Pogba a kan Yuro miliyan 100

Kulob din Manchester City na Ingila ya fara zawarcin dan kwallon tsakiya a kulob din Jubentus da ke Italiya Paul Pogba a kan zunzurutun Yuro miliyan 100 kwatankwacin Fam miliyan 73.8. Rahoton da kafar watsa labaran wasanni ta Gazetteta dello Sport ta kalato a shekaranjiya Laraba ya nuna kulob din Real Madrid na Sifen da kuma na Paris Saint Germain (PSG) su ma sun shiga sahun masu zawarcin dan kwallon a karshen kakar wasa ta bana.

Bayern Munich kuma tana zawarcin Griezmann da berrati
Kocin Guardiola ya ce ya fara yunkurin saye ’yan kwallon Atletico Madrid Antoin Griezmann da kuma na PSG Marco berratti a karshen kakar wasa ta bana don maye gurbin ’yan kwallonsa irin su dabi Alonso da Schweinsteiger da Ribery da kuma Arjen Robben da suka tsufa. Kafar watsa labarin wasani ta Sport Bild ne ta ruwaito wannan labari a shekaranjiya Laraba.

Gasar UEFA Champions League: Jubentus ta jefa Madrid cikin tsaka-mai-wuya
A ranar Talatar da ta gabata ne kulob din Jubentus na Italiya ya doke na Real Madrid da ke Sifen da ci 2-1 a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da (UEFA Champions League) a wasa zagaye na farko. Wannan ci da aka yi wa Madrid shi ye jafeta a cikin matsala don haka tilas ne kulob din ya doke na Jubentus a wasa zagaye na biyu idan suka sake haduwa a ranar Laraba mai zuwa. Kuma daga nan ne za a tantance kungiyar da za ta haye matakin karshe a gasar.

…Yayin da FC Bacelona ta yi wa Bayern Munich sakiyar da ba ruwa
A shekaranjiya Laraba ne kulob din FC Barcelona na Sifen ya yi kaca-kaca na da Bayern Munich da ke Jamus a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) bayan ya doke shi da ci 3-0 a wasa zagayen farko.
Lionel Messi ne ya jefa kwallaye biyu kafin daga bisani Neymar ya zura kwallo ta uku a ragar Bayern.
A ranar Talata mai zuwa ce FC Barcelona za ta bi Bayern Munich gida, watau Jamus don yin wasa zagaye na biyu da hakan zai tantance kungiyar da za ta haye matakin karshe a gasar.
Masu sha’awar kallon kwallo suna ganin FC Barcelona ta yi wa Bayern Munich sakiyar da ba ruwa, don abu ne mai wuya a ce Bayern ta iya fanshe cin da aka yi mata na kwallaye uku babu ko daya.

Kulob din Ajad ya jefi tsuntu uku da dutse daya
Kulob din Ajad da ke Holland ya samu nasarar saye matashin dan kwallo Nemanja Gudeji bayan ya sanya mahaifinsa da kuma wansa a cinikin. Yayin da kulob din ya dauki Nemanja a matsayin mai buga masa kwallo a matakin manya mahaifinsa mai suna Neboisa kuma an dauke shi aiki ne a wani bangare na kulob din shi kuma wansa Dragi kulob din ya tura shi bangaren matasan ’yan kwallo ne a kulob din.

Jaridar De Telegaaf ce ta ruwaito wannan labari.