A tallafa wa Buhari da addu’a – Gwamna Yari

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ya nemi malaman kasar nan su gudanar da addu’a ta musamman ga zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari saboda halin da ya tsinci kansa a halin yanzu. Gwamna Abdul’aziz Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah da na kungiyar […]

A tallafa wa Buhari da addu’a – Gwamna Yari
A tallafa wa Buhari da addu’a – Gwamna Yari

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ya nemi malaman kasar nan su gudanar da addu’a ta musamman ga zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari saboda halin da ya tsinci kansa a halin yanzu.

Gwamna Abdul’aziz Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah da na kungiyar Fityanul Islam suka kai masa gaisuwar murnar sake zabensa a karo na biyu a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
Gwamna Yari ya ce gudanar da wannan addu’a za ta taimaka gaya domin a roki Allah Ubangiji Ya rika masa, domin wasu suna daukar zababben Shugaban kasar kamar wani da Allah Ya aiko ya sauya duk kan al’amari, alhali ba haka lamarin yake ba.
Ya kara da cewa akwai wadanda za su yi ta kokarin ganin hakarsa ta kudirin gyara kasar nan ba ta cimma ruwa ba.
Shugabannin kungiyoyin na Izala da na Fitiyanu wadanda suka fito daga jihohin Sakkwato da Zamfara, sun kai wa Gwamna Yari gaisuwar murnar samun nasarar zaben Gwamnan ne karo na biyu, wanda aka gudanar mako biyu da suka gabata.