A tanadi tsaro na musamman albarkacin bikin Sallah a Kano — Sarki Aminu Bayero

Wasiƙar Sarki Aminu Bayero ta bayyana jadawalin shagulgulan da za a gudanar.

A tanadi tsaro na musamman albarkacin bikin Sallah a Kano — Sarki Aminu Bayero

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero

Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya buƙaci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya yi tanadin tsaro na musamman albarkacin shagulgulan bikin Sallah da ke ƙaratowa.

Sarkin ya miƙa wannan buƙatar ce a cikin wata wasiƙa mai lamba HRH/ADM/06/1/217 da ke ɗauke da kwanan watan 10 ga watan Yunin 2024 wadda sakatarensa ya sanyawa hannu.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Sarkin ya aike da goron gayyata zuwa ga sauran sarakunan gargajiya da su soma shirye-shiryen bikin Sallah

Wasiƙar ta kuma kafa hujjar miƙa wannan buƙatar tana mai amfani da umarnin da kotu ta bayar na kowane ɓangare ya tsaya a matsayarsa dangane da taƙaddamar Masarautar Kano da ke hannun mahukunta na shari’a.

Wasiƙar wadda Galidiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya sanyawa hannu, ta buƙaci a yi tanadin tsaro na musamman albarkacin bikin Sallah Babba wadda za a soma tun daga ranar Lahadi, 16 ga watan Mayun 2024.

Ta kuma bayyana cewa za a soma shagulgulan ne daga Ƙaramar Fadar da ke Nasarawa wadda ta bayyana ƙarara a matsayin wani rukuni na al’ada da addini da ke tara ɗimbin jama’a daga ciki da wajen Kano.

Kazalika, wasiƙar ta zayyana jadawalin shagulgulan da za a gudanar da suka haɗa da Hawan Idi a farfajiyar Masallacin Idi da ke Ƙofar Mata.

Sai kuma Hawan Daushe da zai gudana da misalin ƙarfe 4:00 na rana washegari Litinin, 17 ga watan Yuni.

A ranar Talata, za a gudanar da Hawan Nasarawa da tun daga misalin ƙarfe 8:00 na safe.

Sai kuma Hawan Zagayen Gari da zai gudana daga ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Alhamis.

Wannan buƙatar dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tun bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuɓe wa Sarki Aminu Ado Bayero rawani kuma ya mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karagar Gidan Dabo.

Gwamnan ya yi hakan ne bayan ya rattaba hannu kan dokar rushe masarautun Kano biyar da Majalisar Dokokin Kano ta zartar, wadda aka ƙirƙiro a Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos