A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari?
Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ya dace a tattauna batun – […]
Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Ya dace a tattauna batun – Malam Musa Shaihi
Malam Musa Haruna Shaihi: “Ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a zauren taron makomar kasa da ake gunadarwa. Dalilin da ya sanya ni goyon bayan haka shi ne, saboda ’yan Kudu suna ta yin barazanar wai a raba kasar, don haka ya dace a tattauna domin a gano bakin zaren. Da suke ganin wai don suna da fetur ne suke so a raba, wannan mai sauki ne, domin kafin a samu fetur din ai mu muna da noma da kiwo. Kuma ’yan Arewa ba ci-ma-zaune ba ne. Duk Najeriya ba wanda za ka iya ba jarin Naira dubu daya, ya sarrafa ta, ya samar wa kansa da iyalinsa abinci, sai dan Arewa.”