A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 1

Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa: kwarai kuwa, ya dace a tattauna […]

A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 1
A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 1

Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

kwarai kuwa, ya dace a tattauna batun – Alhaji Usman Babangida

Alhaji Usman Babangida, Kasuwar Malumfashi: “kWarai kuwa, ya dace a tattauna batun rugujewar Najeriya a taron makomar kasa da ke gudana a yanzu saboda wadannan dalilai: Shi makaho idan yana kashi bai san ana ganinsa ba sai an taba shi. Idan an tattauna wannan batu ne za a iya gano mene ne amfanin Arewa da Yamma, mene ne amfanin Kudu da Gabas. Idan an tattauna ne za a gano cewa wane bangare ne zai dogara da kansa? Duk duniya dai babu abin da ya kai abinci muhimmanci a rayuwa. Muna da kasar da za mu noma isasshen abinci. Muna da ma’adanai, kai hatta fetur din ma muna da shi. Babbar matsalarmu a Arewa, ita ce ta rashin kyakkyawan shugabanci. Idan aka raba kasar kuma muka dace da shugabanni nakwarai, babu abin da za mu rasa, domin komai Allah Ya yi mana.