A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 2
Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Bai dace a tattauna batun ba […]
Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Bai dace a tattauna batun ba – Hamisu danmudi
Alhaji Hamisu danmudi Mai Adashi: “A’a, kwata-kwata bai dace ba a tayar da batun, domin yana da kyau kasa ta zama a hade; sai na lura ana yi waArewa rashin adalci wajen raba arzikin kasa. Idan ba za a yi adalci ba, to gara kowa ya kama gabansa shi ya fi.”