A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 3
Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ba na goyon bayan tattauna batun […]
Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Ba na goyon bayan tattauna batun – Musa Yakubu
Alhaji Musa YakubuYagarmawa: “Ni a nawa ra’ayin sam hakan bai dace ba, domin a misali idan ana hade da juna, za mu fi cin moriyar juna da kuma samun ci gaba ta kowane fanni ga al’ummar kasa da kuma ita kanta. Dubi kasar Amurka mana mai yawan johohi 50, kansu hade yake sai ci gaba suke yi kullum. To mu ma hakan idan har za mu ci gaba da zama dunkule kasa daya.”