A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 4

Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Bai dace ba – Maryam Yusuf […]

A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 4
A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 4

Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Bai dace ba – Maryam Yusuf

Maryam Yusuf: “Gaskiya bai dace a a tattauna batun raba Najeriya a taron kasa ba saboda ba zai zama alheri ba ga kasarmu kuma zai janyo bore a kasa saboda haka nake ganin bai kamata a ce an kawo batun ba balantana a tattauna shi a taron. Ya kamata mahalart taron su tattauna duk wani abu da zai kawo hadin kan kasa, su yi watsi da duk wani batu da zai raba kasa.”