A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 5

Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Bai kamata ba – Sada Rabe […]

A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 5
A tattauna batun wargajewar Najeriya a taron kasa ko a bari? 5

Wannan shi ne mako na uku da fara gudanar da taron tattauna makomar kasa a Abuja. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a tattauna batun wargajewar Najeriya a taron ko kuwa a bari? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin al’umma daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Bai kamata ba – Sada Rabe Katsina

Sada Rabe Katsina: “Ni a ganina bai kamata a tattauna duk wani batu da zai raba kasar Najeriya ba saboda Najeriya kasa ce da ta hada mutane da kabilu daban-daban. Kamata ya yi mahalarta taron su mayar da hankali kan abubuwan da za su kawo mana ci gaba da bunkasar tattalin arziki da zaman lafiya a kasa.”