A tausaya wa masu sana’a a Abuja
Editan Aminiya ka ba ni dama in mika kukan matasan masu sana’a ga gwamnati, musamman jin cewa daga manufofinta na gyran kasa a kwai samar da ayyukan yi ga matasa. To, matasa da ke kasuwanci ko tallace-tallace a babban birnin tarayya Abuja na karawa da masu kame, wadanda aka fi sani da ’yan Task force, […]
Editan Aminiya ka ba ni dama in mika kukan matasan masu sana’a ga gwamnati, musamman jin cewa daga manufofinta na gyran kasa a kwai samar da ayyukan yi ga matasa. To, matasa da ke kasuwanci ko tallace-tallace a babban birnin tarayya Abuja na karawa da masu kame, wadanda aka fi sani da ’yan Task force, inda sukan kama matashi mai talla, su kwace kayansa, su kuma yanaka masa haraji. Wani kuma yana iya yin asarar daukacin abin da ya mallaka a hannun ’yan tsaskforce. Shin ba a samar wa matasa abin yi ba, anya kuwa za a iya hana su sana’a? Kuma ’yan sandan da suke yawo da su, ai ba barayi suke kamawa ba. Don haka ko dai a sama mana wuraren sana’a da aka amince mu yi zirga-zirga, ko kuma mu yanke cewa babu tausayin talakan da ya yi kokarin sama wa kansa abin yi, amma na bi, ana kwacewa tamkar barawo. Lallai akwai bukatar gwamnati ta samar da maganin wannan matsalar, yadda matasa za su tabbatar an yi musu adalci, a matsayinsu na ’yan Najeriya. Manufofin da Gwamnatin Buhari ta APC ke son cimmawa sun hada da samar da aikin yi ga matasa da tsaro. To idan matashi ya samu abin yi ba a hantare shi ba, ai kuwa an smau tsaro. Mahukunta a duba wannan lamari. Allah Ya sa mu dace. Daga Sale Iliyasu Babawo, Balan, Kabo, Jihar Kano. 08036753505