A wanke rakumi a wajen wankin mota don ya kara tsada
A birnin Hail da ke kasar Saudiyya, wani mutum ya kai rakuminsa an wnake shi a wurin wanke motoci, inda ya biya Riyal 50, kimanin Naira dubu uku. Ganin yadda ake fesa wa wannan rakumi ruwa, sai al’amarin ya dauki hankali masu wucewa, kamar yadda jaridun Okaz da Saudigazette suka ruwaito. Mutane sun tsaya suna […]
A birnin Hail da ke kasar Saudiyya, wani mutum ya kai rakuminsa an wnake shi a wurin wanke motoci, inda ya biya Riyal 50, kimanin Naira dubu uku. Ganin yadda ake fesa wa wannan rakumi ruwa, sai al’amarin ya dauki hankali masu wucewa, kamar yadda jaridun Okaz da Saudigazette suka ruwaito.
Mutane sun tsaya suna kallo, su kuwa masu aiki, suka ci gaba da aikin da aka sanya su. Masu kallo suka ci gaba da sharhi, ind awasu ke ganin rakumin na cike da farin ciki a duk sa’adda aka fesa masa ruwa ya jike.
Daga bisani mai rakumi, wani manomi ne, wanda ya bayyana cewa ya biya kudinsa har Riyal 50, a wanke masa rakumin don ya kara tsada ne.