A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Bashin da ake bin Nijeriya zai ƙaru zuwa tiriliyan N138 a yayin da Shugaba Tinubu ke shirin ciyo ƙarin bashin tiriliyan N1.8

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Bashin da ake bin gwamantin Nijeriya zai ƙaru zuwa Naira tiriliyan 138 a yayin da Shugaba Tinubu ke neman amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin ciyo ƙarin bashin Naira tiriliyan 1.8.

A wata 19 da zuwa yanzu Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a bisa mulki, gwamnatinsa ta ciyo bashin da ya haura Naira tiriliyan 50, wanda ya zarce rabin wanda ta gada.

A yanzu haka bashin Naira tiriliyan 136 ake bin Nijeriya wanda idan majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo bashin Dala biliyan 2.2 daga ƙasashen waje, yawan kuɗin zai ƙaru zuwa tiriliyan 138.

A ranar Talata Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da takwaransa na Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen takardar neman amincewarsu da karɓo bashin.

Wasiƙar ta bayyana cewa za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen za a karɓo ne wajen cike giɓin Naira tiriliyan 9.17 da aka samu wajen aiwatar da kasafin shekarar nan ta 2024.

Wasiƙar ta bayyana cewa karɓo bashin ya dace da tanadin Dokar Hukumar Kula da Basuka ta Ƙasa (DMO) ta  2003, kuma ta riga ta samu amincewar Majalisar Zartaswa ta Tarayya.

Sabon bashin na 2024 ya kai Naira tiriliyan N7.83, wanda ya ƙunshi bashin cikin gida na tiriliyan N6.06 da kuma bashin ƙasashen waje na tiriliyan N1.77.

Tinubu ya ba da shawarar biyan basukan ta hanyar takardun lamuni na Eurobonds, ko Sukuk ko kuma bashin Bridge Finance/Syndicated Loans.

Da yake magana kan kamarin bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce samu Eurobond da  Sukuk na Dala biliyan 1.7 da dala miliyan 500, sun nuna yadda ƙasashen duniya suka yi na’am da Gwmanatin Tinubu domin aiwatar da ayyukan cigaban tattalin arziki.

Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan N50 a wata 19

A lokacin da Tinubu ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayu , 3023, bashin Naira tiriliyan N87.3 ake bin gwamnatin Nijeriya.

Zuwa watan Yunin 2024, yawan basukan ya ƙaru zuwa tiriliyan N134.

Hakan na nufin a cikin shakara guda gwamnatin ta ciyo ƙarin bashin tiriliyan N46.7, wanda ya zarce rabin abin da ta gada.

Idan aka hada jimillar basukan a tsawon wata 19 da shugaban ya yi a kan mulki yawan basukan da gwamnatin ta ciyo ya haura tiriliyan 50.