A wata 6, Najeriya ta kashe tiriliyan 2.34 wajen biyan bashi – DMO

Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ne ya tabbatar da haka a wani rahoto

A wata 6, Najeriya ta kashe tiriliyan 2.34 wajen biyan bashi – DMO

Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce Najeriya ta kashe Naira tiriliyan 2 da biliyan 340 wajen biyan bashi a cikin wata shida na farkon 2023.

Wani sabon rahoton ofishin ya nuna cewa a watanni uku na biyun shekara ta 2023 zuwa biliyan 849.58.

Hakan dai na nuna raguwa da kimanin kaso 43.04 cikin 100 daga tiriliyan 1.49 din da aka kashe wajen biyan bashin a watanni uku na farkon 2023.

Alkaluma daga ofishin dai sun nuna a watanni ukun farkon 2023, Najeriya ta ware Naira biliyan 874 domin biyan basussukan cikin gida, sai Dalar Amurka miliyan 801.36 (kwatankwacin Naira biliyan 617.35) domin biyan basukan waje, jimillar Naira tiriliyan 1.24 ke nan.

A baya dai Najeriya na kasafta kowacce Dalar Amurka a kan Naira 770.38 wajen biyan bashin.

Bugu da kari, sabanin a bara da kasar ta ware kusan Dala miliyan 131 domin biyan basussukan bankin Exim na kasar China a watanni uku na biyu a 2023, DMO ya ce ko kwabo ba a ware ba domin biyansu a watanni uku na farkon shekarar.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano