A watan Disamba za a gudanar da zaben kananan hukumomin Yobe
A karo na biyu gwamnatin Jihar Yobe ta sake sa lokacin da za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar inda ta ajiye watan Disamban da ke tafe sakamakon kyautatuwar harkokin tsaro da kammala dunkulewar jam’iyyun adawa zuwa Jam’iyyar APC.Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika mukullan […]

A karo na biyu gwamnatin Jihar Yobe ta sake sa lokacin da za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar inda ta ajiye watan Disamban da ke tafe sakamakon kyautatuwar harkokin tsaro da kammala dunkulewar jam’iyyun adawa zuwa Jam’iyyar APC.
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika mukullan motoci 19 kirar TOYOTA HILUd ga Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Alhaji Muhammad Jauro Abdu a Damaturu.
Gwamna Gaidam ya ce tun a watan Yuni da ya gabata ne gwamnatin jihar ta yi niyyar gudanar da zaben kananan hukumomin amma kasancewar ana kokarin dunkulewar jam’iyyun adawar ya sa aka dage zaben, kuma ganin yanzu komai ya kammalu da kuma kyautatuwar harkokin tsaro a a jihar ne aka sanya watan Disamba ko makon farko na shekarar 2014 don gudanar da zaben kananan hukumomin.
Ya ci gaba da cewa yana da yakinin hukumar zabe ta jihar (SIEC) za ta iya gudanar da zaben ganin tuni an samar da akwatunan kada kuri’un da za a yi amafani da su a yayin zaben da sauran kayayyakin da suka kamata.
Gwamnan ya kirayi hukumar ta tabbatar ta kula da motocin da aka samar mata ta yadda ba za a samu matsaloli ba dangane da harkokin sufuri kafin zabe da yayin gudanar da shi.
A wani labarin kuma hukumar zaben ta Jihar Yobe ta bayyana ce ta shirya tsafa don gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 28 ga watan Disamban da ke tafe.
Da ya ke bayani ga ’yan jaridu bayan kammala taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe da kuma jam’iyyun siyasa, shugaban hukumar Alhaji Muhammad Jauro Abdu ya ce hukumarsa ta shirya tsaf don gudanar da zaben kamar yadda gwamnatin jihar ta ba da umarni.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe Alhaji Sunusi A. Rufa’i ya ce rundunarsa a shirye take ta ba da tsaro mai inagnci don ganin an samu nasara gudanar da zaben kananan hukumomi cikin kwanciyar hankali.
Jam’iyyun siyasa bakwai ne za su shiga a dama da su a zaben da suka hada da Jam’iyyar APC mai mulkin jihar da PDP da sabuwar Jam’iyyar PDM.