A watan gobe za a fara gasar Firimiya ta Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce akwai yiwuwar a fasar gasar rukuni-rukuni na Najeriya a watan gobe, kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta Africanfootball.com ta kalato.Hukumar ta ce ta yi haka ne don ba kungiyoyin kwallon kafar da za su fafata a gasar Zakarun Kulob-Kulob na Afirka (Champions League) da kuma wacce […]

A watan gobe za a fara gasar Firimiya ta Najeriya
A watan gobe za a fara gasar Firimiya ta Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce akwai yiwuwar a fasar gasar rukuni-rukuni na Najeriya a watan gobe, kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta Africanfootball.com ta kalato.
Hukumar ta ce ta yi haka ne don ba kungiyoyin kwallon kafar da za su fafata a gasar Zakarun Kulob-Kulob na Afirka (Champions League) da kuma wacce za ta fafata a gasar cin Kofin kalubale na Afirka (Confederation Cup) damar shiryawa sosai.
Kulob din Enyimba na Aba zai fafata a gasar Zakarun Kulob na Afirka yayin da Warri Wolbes kuma zai fafata a gasar cin Kofin kalubale na Afirka.
“Za mu fara gasar da wuri ne don mu ba kulob-kulob din da za su wakilci Najeriya a gasanni daban-daban da za a fara a watan Fabrairun 2016 damar shiryawa sosai”, inji daya daga cikin jami’an Hukumar NFF wanda bai so a ambaci sunansa.
A shekaranjiya Laraba ne  Hukumar NFF ta amince da watan Janairu a matsayin watan da za a fara gasar Firimiya a taron shekara-shekarar (AGM) da ta yi a Abuja.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa