A watan gobe za a yanke wa tsohon minista Fani Kayode hukunci

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas ta sanya ranar 18 ga watan Yunin bana domin yanke hukunci a shari’ar da ake yi tsakanin hukumar yaki da almundahanar kudi ta EFCC da tsohon Ministan Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Cif Fami Fani Kayode kan zargin sata da almundahanar kudin gwamnati. Alkalin kotun, Rita Ofili-Ajumogobia ta bayyana […]

A watan gobe za a yanke wa tsohon minista Fani Kayode hukunci
A watan gobe za a yanke wa tsohon minista Fani Kayode hukunci

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas ta sanya ranar 18 ga watan Yunin bana domin yanke hukunci a shari’ar da ake yi tsakanin hukumar yaki da almundahanar kudi ta EFCC da tsohon Ministan Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Cif Fami Fani Kayode kan zargin sata da almundahanar kudin gwamnati.

Alkalin kotun, Rita Ofili-Ajumogobia ta bayyana ranar yanke hukuncin a ranar Litinin din da ta gabata bayan da ta amince wa lauyoyin hukumar EFFC da lauyoyin wanda ake zargi su gabatar da shaidarsu ta karshe ga kotun.
Shi dai Cif Fani Kayode wanda hukumar EFCC ta gurfanar da shi a shekarar 2008 a kotun mai Shari’a Ramat Muhammed, tana zarginsa ne da satar Naira miliyan 100 a lokacin da yake Ministan Ma’aikatar Al’adu Da Yawon Bude Ido da kuma lokacin da yake Ministan Hukumar Kula Da Sufurin Jiragen Sama.
Daga bisani an rage yawan kudin da ake zarginsa da sata zuwa Naira miliyan biyu da dari daya a ranar 17 ga watan Nuwamban shekarar 20014 bayan da mai shari’a Rita ta yi watsi da zarge-zarge 38 daga cikin zargi 40 din da hukumar EFCC take yi masa saboda rashin kwararan hujjoji.
Lauyan hukumar, Mista Festus Keyamo ya nemi kotun ta yi amfani da hujjojin da aka gabatar mata, ta daure Fani Kayode a gidan kurkuku saboda a cewarsa tsohon ministan ya kasa wanke kansa daga zarge-zargen da ake yi masa.
Lauya Keyamo ya yi nuni da cewa tsohon ministan ya yi tu’ammuli da kudin da suka kai kimanin Naira dubu dari biyar, wanda hakan ya saba wa dokar sata da almundahanar kudi ta Najeriya.
Lauyan ya ci gaba da cewa Fani Kayode ya yi ikirari da kansa a ranar 22 ga watan Disemban shekarar 2008 cewa ya yi tu’ammuli da kudin da ake zarginsa da su.
Dagan nan sai lauyan ya ce hukumar EFCC ta yi aikinta tunda har Fani Kayode ya yi mata ikirarin aikata abin da take zarginsa da yi.
Saboda haka ya ce ya rage ga Fani Kayode ya yi bayani dalla-dalla don wanke kansa daga zargin da ake yi masa. Amma lauyan Fani, Mista Adedayo Adedipe ya musanta cewa wanda yake karewa ya yi ikirarin aikata laifin da ake zarginsa da yi. Ya ce hukumar EFCC ta kasa nuna inda ya ya amince da Naira miliyan daya da ake zarginsa da sata a zarge-zargen da ta yi masa. Ya kara da cewa hukumar EFCC ta kasa nuna wa kotun mutumin da ya baiwa wanda ake zargi kudin.