A yaba wa shugaban da ya kyautata wa al’umma

Duk shugaban da ya kyautata a yaba masa, wanda bai yi ba a fadi ko Allah zai sa ya gyara.  Don haka ina jinjinawa mai girma Shugaban kasa Malam Muhammadu Buhari sakamakon kaddamar da jirgin kasa da ya yi, wanda zai rika jigila tsakanin Abuja da Kano. Samuwar wan nan jirgin kasa zai haifar da […]

A yaba wa shugaban da ya kyautata wa al’umma
A yaba wa shugaban da ya kyautata wa al’umma

Duk shugaban da ya kyautata a yaba masa, wanda bai yi ba a fadi ko Allah zai sa ya gyara.  Don haka ina jinjinawa mai girma Shugaban kasa Malam Muhammadu Buhari sakamakon kaddamar da jirgin kasa da ya yi, wanda zai rika jigila tsakanin Abuja da Kano. Samuwar wan nan jirgin kasa zai haifar da abubuwa kamar haka:
-Tafiya cikin kwanciyar hankali.
-Samar da ayyukan yi.
-Samar da kudin shiga.
-Rage yawaitar hadura.
-Bunkasa harkar kasuwanci a tsakanin ‘yan kasa.
Abubuwan dai da yawa wadanda samar da wannan jirgin kasa zai haifar wa al’ummar Najeriya, musamman ma matasa da ke fama da rashin aikin yi. Ya Allah Ka kara wa Baba Buhari lafiya, Ka ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa na shugabanci amin.
‘Yan majalissa ya kamata ku gane cewa, mu fa ‘yan Najeriya muna kallonku game da duk wata hayaniya da kuke yi. Abin da muke so da ku, shi ne, kowa ya karbi laifinsa, tare da neman afuwa a wajen wadanda suka tura shi majalissar, wato Talakawa. Domin akwai ranar kin dillanci.
Mai son tara dukiya ya bar siyasa, Najeriya ta sauya. Duk mai rike da mukamin gwamnati yana da damar yin murabus, ko kuma idan talakawa sun kasa aminta da shugabancisa, suna da damar yi masa kiranye. ’Yan majalisu suna da damar tsige shugabansu, kama daga shugaban kasa zuwa gwamnoni a jihohi ko shugaban majalisar, matukar shugaban ya gaza matuka a shugabancinsa. Ba a mulki don a tara dukiya, ana yi ne don ciyar da al’umma gaba….
In har Alaramma wane da Malam wane da Alhaji wane da Sarki wane da Gwamna wane da sauransu, ba za su yi farin cikin a ga ‘Yar su na wasan kwaikwayo ba, hakan alama ce da ke nuni ba aikin alkhairi ba ne.
Ba wanda zai so a ce yau ‘yarsa ta shekara sama da 20 bai aurar da ita ba. Ko kuma a ce sama da shekaru talatin ba aure, ya zamto ta kama sana’ar wasan kwaikwayo. ‘Yar mutunci gidan mutunci ba za ta yarda ta rika shiga ta fitsara ba, ba gyale ko hijab, tana rawa a dauke ta a bideo ana sayar wa mutane ba?
Idan har a matsayinka na mutumin kirki ko mu ce malami za ka ce gina Dandalin shirya fina-finan Hausa abu ne mai kyau, to muna fatan a cikin ‘ya’yanka mata sai ka duba wacce ta fi kyau da kamun kai ka sanya ta a harkar film, domin bayar da gudummawarka ga fadakarwar da ka ce ana yi. Zuwa shekara guda in ba sa’a ba sai ka zubda hawaye..
Ambaliyar ruwan sama a cikin garin Hadejia. Duk damina ta na jawo asara mai dumbin yawa, muna fatan gwamnati za ta share mana kukanmu.Ga wasu abubuwan da ke jawo mana ita:
-Rashin magudanan ruwa a wadace.
-Cike wasu ramuka da ke daukar ruwa a lokacin damina ba tare an yi manyan kwalbati a wajen ba.
-Akwai unguwanni da babu kwalbatin ma, haka ruwa zai cika layuka har damina ta wuce.. Wadannan na daga cikin abubuwan da ke jawo mana ambaliyar. Duk wanda ya san Hadejia zai gaskata zance na.
*Ina kira ga matasa don Allah Mu guji cin mutuncin mutane musamman shugabanninmu a shafukan sadarwa irin su facebook, Whatsapps da Twitter da sauransu. Domin kuwa yanayin rubutunka shi ke nuna irin tarbiyarka. Allah Ya sa mu dace.
Nasiru Kainuwa Hadeja 08100229688. [email protected]