A ’yan takarar shugabancin Najeriya babu kamar Kwankwaso – Maigado
Shugaban kungiyar Kwankwasiya reshen Jihar Filato Alhaji Nuradeen Inuwa Maigado Takai ya ce a duk ’yan takarar shugabancin kasar nan da suka fito babu wanda ya kai cancantar da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso yake da ita.Alhaji Nuradeen Maigado ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, bayan da ya […]
Shugaban kungiyar Kwankwasiya reshen Jihar Filato Alhaji Nuradeen Inuwa Maigado Takai ya ce a duk ’yan takarar shugabancin kasar nan da suka fito babu wanda ya kai cancantar da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso yake da ita.
Alhaji Nuradeen Maigado ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, bayan da ya karbi wasu sababbin ’yan kungiyar daga wasu kananan hukumomin jihar.
Ya ce abin da ya sa suke ganin Gwamna Kwankwaso ya fi sauran cancantar ya jagoranci kasar nan, shi matashi ne kuma ba ya da tsoro kuma ya san harkokin tsaron kasar nan saboda ya yi Ministan Tsaro.
Ya ce bayan haka a halin yanzu babu jihar da ta ci gajiyar mulkin dimokuradiyya a Najeriya, kamar Jihar Kano saboda ayyukan raya kasa da Kwankwaso ke gudanarwa. “Don haka muke ganin idan Kwankwaso ya zama Shugaban kasa talakawan Najeriya za su huta. Kuma mu a Jihar Filato wannan tafiya ta Kwankwasiya ta samu karbuwa,” inji shi.
Ya ce, a farkon tafiyar kashi 90 na wadanda suke goyon bayansa, Hausawa ne da Fulani, amma zuwa yanzu sun samu kabilu daban-daban na jihar nan daga kananan hukumomin Jos ta Gabas da Bassa da Langtang da Shendam da Mangu da Bokkos da Mekang da sauransu da suke marasa masa baya.