’A yanke min hukuncin rataya a bainar jama’a’

Wani matashi mai shekara 22, ya roki a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama bisa zargin garkuwa da wani matashi a Jihar Kano. Wanda ake zarin ya nemi a ba shi Naira miliyan 1.3 da katin waya na dubu 20 domin fansar wanda ya sace din. Ba a ware wa tashar […]

’A yanke min hukuncin rataya a bainar jama’a’

Wani matashi mai shekara 22, ya roki a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama bisa zargin garkuwa da wani matashi a Jihar Kano.

Wanda ake zarin ya nemi a ba shi Naira miliyan 1.3 da katin waya na dubu 20 domin fansar wanda ya sace din.

“Don Allah, don Annabi jama’a ban taba yi ba, amma ina rokon Gwamnatin Jihar Kano don Allah, don Annabi a yanke min hukuncin kisa a gaban jama’a, don Allah a rataye ni, don Allah don Annabi shi ne nake bukata”, inji shi a lokacin da ake gabatar da shi.

Ya ce ya yi garkuwa da mamacin ne bayan ya yi masa wayo ya kai shi kauyen Borodo Harin Gwarmai a Karamar Hukumar Bebeji.

Daga nan sai ya kai mamacin gona soboda rashin inda zai kai shi, a nan ne kuma ya kashe shi.

“Bayan na tafi da shi gona, sai na shake masa wuya na kashe shi, bayan na kashe shi sai na haka rami na binne shi.

“Sai da na dauki kwana uku ni kadai ina kokarin yadda zan yi da shi, daga bisani na haka rami na binne shi”, kamar yadda ya shaida wa ’yan sanda.

Ya yi bayanin ne ne a lokacin da jami’an ’yan sanda suka tafi da shi wurin da ya binne gawar mamacin da ya amsa cewa ya kashe.

Ya kara da cewa: “Don Allah a roka mun gafara wurin baban yaron nan ya yafe mun don Allah, don girman Allah jama’a”.

Da yake jawabi a wurin tono mamacin, Kakain Rundunar ’Yan Sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ranar 9 ga Nuwamba, 2020, wani mutum mai suna Alh. Kabiru ya kawo rahoto cewar an yi garkuwa da dansa mai suna Tijjani.

Ya ce: “Tun lokacin da muka samu rahoton Kwamishinan ’Yan Sanda ya ba mu umarnin gudanar da bincike na tsawon sati biyu”.

Kiyawa ya ce bayan sun dauki kusan mako biyu suna gudanar da bincike ne suka yi sa’ar kamo wanda ake zargi da aikata laifin.

Ya ce kawo yanzu haka rundunar ta kammala bincike za kuma ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano