A yau hukumar zabe zata fitar da sunayen ‘yan takarar Gwamnoni
A yau Alhamis ne hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata fitar da jadawalin sunayen ‘yan takarar Gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da ‘yan takarar mazabun babban birnin tarayya Abuja wanda za a yi ranar 2 ga Maris 2019. Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan kuma ya ce, […]
A yau Alhamis ne hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata fitar da jadawalin sunayen ‘yan takarar Gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da ‘yan takarar mazabun babban birnin tarayya Abuja wanda za a yi ranar 2 ga Maris 2019.
Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan kuma ya ce, za a sanar da sunayen a reshen ofisoshin hukumar zaben na jihar a duk jihohin kasar da kuma shafin intanet na hukumar.
Za a gudanar zaben Gwamnoni 29 a cikin jihohi 36 na kasar.